Amurka ta karrama Limamin da ya tsiratar da Kiristoci 300 a Filato

Amurka ta karrama Limamin da ya tsiratar da Kiristoci 300 a Filato

Hukumar kasar Amurka a Najeriya ta yabi Imam Abdullahi Abubakar, limamin da ya ceto dururuwan Kiristoci a lokacin da makiyaya suka kai musu hari a jihar Filato a ranar 23 ga watan Yuli, 2018.

Abubakar, Babban limamin kauyen Nghar a yankin Gashish a jihar Filato, ya samu yabo bayan ya nema wa wasu da makiyaya suka yi yunkurin kai ma hari mafaka a masallaci.

A shafin twitter, ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ta mika lambar yabo ga Abubakar, Tauraron Najeriya.

Ofishin jakadancin ta bayyana limamin dan shekara 84 din a matsayin “mai son zaman lafiya” wanda ya sanya imaninsa a mataki” wajen bada tsaro ga rayukan mutanen da ba addininsu guda ba.

Amurka ta karrama Limamin da ya tsiratar da Kiristoci 300 a Filato

Amurka ta karrama Limamin da ya tsiratar da Kiristoci 300 a Filato
Source: UGC

Yace: “Na boye matayen a gida na sannan bayan haka, na boye mazajen a masallaci.

KU KARANTA KUMA: Takarar neman shugabancin majalisa da nake ya samo asali ne daga abokan aikina – Lawan Ahmed

Har ila yau, yan ta’addan sun cafke limamin, inda suka tilasta shi akan ya fitar da wadanda ba musulmai ba daga masallacin.

Amman malamin yace ya yaudari yan bindigan ne kan cewa dukkan wadanda ke a masallacin musulmai ne, daga jin haka, yan bindigan suka yi tafiyan su inda suka cigaba da kashe kashe.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel