Majalisar dattijai ta tabbatar da hadimar Buhari a matsayin shugabar hukumar NDC

Majalisar dattijai ta tabbatar da hadimar Buhari a matsayin shugabar hukumar NDC

A ranar Alhamis ne majalisar dattijai ta tabbatar da Abike Dabiri-Erewa, hadimar shugaba Buhari, a matsayin shugabar hukumar Najeriya mai kula da 'yan kasar dake zaune a kasashen ketare (NDC), wacce a turance ake kira 'Nigerian Diaspora Commission'.

Mambobin majalisar sun tabbatar da Abike bayan amincewa da rahoton kwamitin majalisar a kan kungiyoyin da ba na gwamnati ba, wanda sanata Rose Oko (dan jam'iyyar PDP daga jihar Kuros Riba) ke jagoranta.

Kafin tabbatar da ita a matsayin shugabar hukumar NDC, Abike ta kasance mai taimaka wa ta musamman ga shugaba Buhari a kan harkokin kasashen ketare.

Shugaba Buhari ne ya mika sunanta ga majalisar a shekarar 2018 domin tabbatar da ita a matsayin shugabar hukumar NDC.

Majalisar dattijai ta tabbatar da hadimar Buhari a matsayin shugabar hukumar NDC
Shugabar hukumar NDC; Abike Dabiri-Erewa
Source: Depositphotos

Toshuwar 'yar jarida, Abike ta taba zama mamba a majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ikorodu daga shekarar 2003 zuwa 2015.

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar Umar Gonto, gogaggen masanin ilimin shari'a, ya zama sabon babban darektan gudanar wa na hukumar gidajen gwamnatin tarayya (FHA).

DUBA WANNAN: Bayan 'sa hannun' Ganduje: Jerin kananan hukumomin dake karkashin masarautun Kano 5

Nadin Gonto ya biyo bayan karewar zangon shugaban hukumar FHA, Mohammed Al-Amin, a ranar 6 ga watan Mayu.

Wani jami'i a ma'aikatar aiyuka, gidaje da lantarki da ya nemi a boye sunan sa, ya ce an bi dokokin tsarin mulkin Najeriya da na aikin gwamnati wajen nadin Gonto. Ya ce Gonto ya zama shugaba ne kasancewar shine babban jami'i a hukumar bayan karewar zangon Al-Amin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel