Binciken EFCC: PDP na zargin APC da kullawa Saraki tuggu

Binciken EFCC: PDP na zargin APC da kullawa Saraki tuggu

Ba ya ga yin Allah wadai, jam'iyyar adawa ta PDP na zargin gwamnatin jam'iyya mai ta APC da sabunta tuggu da kulla wata kitirmurmura da manufa ta cin zarafi da wulakantas da shugaban majalisar dattawan Najeriya, Abubakar Bukola Saraki.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, jam'iyyar ta yi babatu cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 8 ga watan Mayun 2019 da sanadin kakakin ta, Mista Kola Ologbondiyan a babban birnin kasar nan na tarayya.

Kakakin jam'iyyar PDP na kasa, Mista Kola Ologbondiyan

Kakakin jam'iyyar PDP na kasa, Mista Kola Ologbondiyan
Source: UGC

Cikin sanarwar da Ologbondinyan ya gabatar ya bayyana cewa, ko shakka babu yunkurin hukumar hana yiwa tattalin arziki ta'annati ta EFCC wajen aiwatar da bincike a kan shugaban majalisar dattawa wata kitirmurmura ce da tirka-tirka irin ta siyasa.

Ologbondiyan ya ke cewa, sabunta wannan lamari na gudanar da bincike a kan Saraki ya yi daidai da kudirin gwamnatin jam'iyyar APC na dankwafar da dukkanin jiga-jigan 'yan siyasa masu adawa da ita a siyasance.

KARANTA KUMA: Fati Washa ta samu mabiya Miliyan 1 a shafin Instagram

Jam'iyyar PDP ta bayyana mamakin ta kwarai da aniyya dangane da yadda kotun kolin kasar nan ta tsarkake Saraki daga dukkanin tuhumce-tuhumce da shimfidar zargi na almundahana da karkatar da dukiyar al'umma.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar EFCC a makon da ya gabata ta sake bude sabon shafi na gudanar da bincike a kan shugaban majalisar dattawan kasar nan yayin kasancewar sa gwamnan jihar Kwara a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel