EFCC ta cafke dan majalisa akan laifin damfara Malaman makaranta naira miliyan 4 (Hoto)

EFCC ta cafke dan majalisa akan laifin damfara Malaman makaranta naira miliyan 4 (Hoto)

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta sanar da kama wani dan majalisa dake wakiltar mazabar Malete/Ipuru a majalisar dokokin jahar Kwara, Honorabul Adebayo Muhammad da laifin damfara wasu Malaman makaranta.

Legit.ng ta ruwaito Muhammad ya damfari Malaman makarantar ne naira miliyan hudu (N4,000,000) da sunan ya sayar musu da wani fuloti, a shekarar 2015, ashe wannan Fuloti ba nasa bane, tsabagen damfara ce kawai.

KU KARANTA: Babu zato babu tsammani aka zabeni – Sabon kaakakin majalisar dokoki

EFCC ta cafke dan majalisa akan laifin damfara Malaman makaranta naira miliyan 4 (Hoto)

Muhammad
Source: Facebook

Abinka da kwararren madamfari, har takardar rasidi ya baiwa Malaman makarantar shaidar cewa ya sayar musu da filinsa, sai dai bayan cinikin ta tashi, Malaman sun gano cewa damfararsu yayi, sun nemi ya biyasu kudinsu, amma Muhammad ya dinga musu wala wala.

Haka ne yasa Malaman da suka hada da Mary Kolade, Ezekiel Babatunde, Felicia debiyi, Grace Awolola, Julius Omole da Abiodun Balogun suka garzaya ofishin EFCC dake garin Ilorin don kai korafi, inda suka bayyana cewa sun gano dilin mallakin ma’aikatar gidaje da sifiyon Najeriya ne.

A yanzu haka EFCC ta yi ram da dan majalisar, kuma tana gudanar da cikakken binciken kwakwaf akansa da nufin gurfanar dashi gaban kotu domin samun hukuncin da yayi daidai da laifin daya aikata na damfara, yaudara da zamba cikin aminci.

Abin tambayar shine ta yaya jama’a suka zabi wannan kasurgumin barawo a matsayin dan majalisa, wace mutunci yake dashi da har zai kare musu nasu mutuncin?

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel