Ra’ayoyin 'yan Najeriya kan kirkirar sabbin masarautun Kano

Ra’ayoyin 'yan Najeriya kan kirkirar sabbin masarautun Kano

A ranar Laraba ne gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu a kan sabuwar dokar kafa sababbin masarautu guda hudu da suka hada da Rano da Karaye da Gaya da Bichi.

Sa hannu kan wannan sabuwar dokar zai ba gwamnatin Jihar Kano damar nada sababbin sarakuna na masarautun huda da kuma shata iyakar fadin kasarsu, sannan kuma shi Sarkin Kano na yanzu Muhammadu Sanusi II zai zama Sabon Sarkin Birnin Kano da Kewaye.

Sai dai wannan ya haifar da samun mabanbantan ra'ayoyi daga jama'a daban-daban a fadin Najeriya.

A wani neman jin ra'ayoyin mutane da sashen Hausa na BBC Hausa ya shirya wasu mutane sun bayyana ra'ayoyinsu kamar haka::

''Masarautar Kano masarauta ce mai iko... Kirkirar wasu zai janyo koma bayane ga al'adar bahaushe musamman dan Kano.. Sannan masarautar zata kasance ba ta da iko koh tasiri kuma.''

''Muna goyan bayan wannan tsari na kara masarautu a kano.''

''Wannan siyasa ce kawai ba batun yanci ba ..kuma mu dai bamu goyan bayan sa.''

Wani mutum kuma yace ''to ai shi ma Sarki Sanusin siyasa ce ta sa ya zama Sarki, in ban da siyasa da yanzu Sunusi Ado Bayero shi ne Sarki.''

KU KARANTA: Kafa Hukumar Bunkasa Arewa maso gabas: mayar da bukin ruwan kuri’un da aka yi man ne— Buhari

Wasu na ganin wannan rikicin na kasa masarautar gida biyar wani yunkuri ne na rage karfin Sarkin Kano Muhammad Sanusi II wanda ake gani kamar yana yawan sukar manufofin gwamnati.

Amma hukumomi a jihar sun bayyana cewa an kasa masarautar zuwa gida biyar ne domin tabbatar da cewa an kara matso da mutane kusa da sarakuna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewarku tare da mu. Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel