Babu zato babu tsammani aka zabeni – Sabon kaakakin majalisar dokoki

Babu zato babu tsammani aka zabeni – Sabon kaakakin majalisar dokoki

Sabon kaakakin majalisar dokokin jahar Jigawa, Alhaji Idris Garba inkiya Kareka ya bayyana cewa zabarsa da takwarorinsa suka yi a matsayin kaakakin majalisa yazo masa babu zato babu tsammani, inda yace bai taba tsammanin zasu nadashi wannan mukami ba.

Wannan shine karo na biyu da yan majalisun dokokin jahar Jigawa suke zabar Idris Garba a matsayin kaakakin majalisa, bayan sun tsigeshi a karon farko suka maye gurbinsa da Isa Idris Gwaram, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Jama’tu Nasril Islam ta koka ga Buhari game da tabarbarewar tsaro a Najeriya

Babu zato babu tsammani aka zabeni – Sabon kaakakin majalisar dokoki

Idris Garba, Sabon kaakakin majalisar dokokin Jigawa
Source: UGC

Idan za’a tuna a ranar Talata, 7 ga watan Mayu ne aka dambace a majalisar dokokin jahar Jigawa bayan barkewar rikici tsakanin yan majalisun wanda har ta kai ga an baiwa hammata iska, har ma wasu suka karya sandan ikon majalisar.

Wannan rikici dai ya samo sila ne yayin da kaakakin majalisar ya bayyana kudurin yin kwaskwarima ga dokar hana duk wani tsohon kaakakin majalisa ko mataimakinsa da aka taba dakatarwa ko tsigewa daga sake neman mukamin kaakaki da mataimakin kaakaki.

Furta wannan batu keda wuya sai kawunan yan majalisar ta rabu biyu, yayin da wani bangare ke goyon bayan kudurin, bangare guda kuma ke nuna adawa da kudurin a karkashin jagorancin Abdulrahman Alkassima dake wakiltar mazabar Yan kwashi.

Shi dai dan majalisa Alkassim shine akan gaba wajen kokarin hada kan yan majalisar don ganin sun mayar da tsohon kaakakin majalisar Idris Garba Jahun mukaminsa, sai dai kimanin shekaru uku da suka gabata ne yan majalisar suka tsige Jahun a matsayin kaakaki, don haka kaakakin majalisar mai ci yake yaki da sake komawarsa mukamin.

Abinka da rabo, duk anyi rigimar an kare, kuma tsohon Idris Garba ya sake darewa wannan mukami bayan yan majalisu 20 cikin 30 sun sake zabensa a matsayin jagoransu, kuma ya bayyana godiyarsa a garesu bisa wannan karamci da suka nuna masa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel