Jam’iyar APC reshen jihar Kaduna ta baiwa El-Rufai kariya bisa kalamansa da yayi a Legas

Jam’iyar APC reshen jihar Kaduna ta baiwa El-Rufai kariya bisa kalamansa da yayi a Legas

-Jam'iyar APC ta Kaduna ta karyata zance dake yawo a yanzu cewa El-Rufai yayi kalaman batanci ga Bola Tinubu

-Sakataren hulda da jama'a na jam'iyar a Kaduna Salisu Tanko shine yayi mana fashin bakin akan gaskiyar wannan al'amari

Jam’iyar APC reshen jihar Kaduna ta kare Gwamna Nasir El-Rufai akan kalamansa game da siyasar ubangida a jihar Legas.

A takardar jam’iyar APC reshen jihar Kaduna wacce ta fito daga hannun sakataren hulda da jama’a na jam’iyar, Salisu Tanko Wusono ya fadi cewa yake, “ A jiya tamkar Legas wacce ke ikirarin kuri’a sama da miliyan shida ace ta samu kuri’ar mutane miliyan daya kacal.” A cewar Salisu.

Jam’iyar APC reshen jihar Kaduna ta baiwa El-Rufai kariya bisa kalamansa da yayi a Legas

Jam’iyar APC reshen jihar Kaduna ta baiwa El-Rufai kariya bisa kalamansa da yayi a Legas
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Majalisar zartarwa ta tarayya ta ware N970.2m domin gina barikin hukumar kwastam

Ga kadan daga cikin abinda takardar ta kunsa “ Reshen APC na jihar Kaduna na kokarin bada goyon baya ga gwamnan jihar Kaduna kan cewar da yayi ko wane mai katin kuri’a yana da yancin zaban ra’ayinsa. Saboda abin sam ba dadi kasancewa jiha mai kuri’a sama da miliya shida ya kasance miliyan daya ne kadai sukayi zabe.

“ A don haka muna tare da gwamnan saboda abinda ya fadi ba komai bane face shawara wacce take daidai, musamman ga masu ruwa da tsaki cikin lamuran zabe na su lura tareda tabbatar da masu dauke da katin zabe sun jefa kuri’unsu a duk inda suke.” A fadar wannan takarda.

Jam’iyar ta kara cewa, ko kadan gwamnan bai zagi jagoran APC a jihar ta Legas ba cewa da Bola Tinubu ko kuma wani mutum na daban kamar yadda yake yawatawa a kafofin sadarwa.

“ Bayan tattaunawar da mukayi tareda masu ruwa da tsaki akan lamarin, mun fahimci cewa babu maganar zagi ko cin mutunci daga baki gwamna El-Rufai. Gwamnan na kokarin fahimtar da mutane ne akan muhimmanci fitowa zabene kawai, kamar yadda ta kasance a zaben kwanan nan.” A cewar sakataren.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel