Sabbin masarautu: Wata kungiya tayi zanga-zanga a Kano

Sabbin masarautu: Wata kungiya tayi zanga-zanga a Kano

Wata kungiya mai suna 'Kano First' tayi zanga-zanga a kan kudirin kirkiran sabbin masarautu hudu a jihar Kano.

'Yan kungiyar sun taru a gidan Muritala dauke da takardu da rubuce-rubuce masu nuna rashin jin dadinsu a kan kudirin da majalisar dokoki na jihar ta amince da shi na kafa sabbin masarautu.

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya rattaba hannu a kan dokar bayan majalisar dokokin jihar ta amince da kudirin dokar a ranar Laraba.

Anyi zanga-zangar kin amincewa da kirkirar masarautu a Kano
Anyi zanga-zangar kin amincewa da kirkirar masarautu a Kano
Source: Twitter

Dokar ta za ta bawa gwamnatin damar rage karfin msarautar Kano bayan ta fitar da wasu masarautu hudu daga tsohuwar masarautar ta Kano.

DUBA WANNAN: An tura 'zauna gari banza' gidan yari saboda taba nonon kwaila

Kungiyar ta bukaci gwamnatin jihar ta mayar da hankali a kan abubuwa masu muhimmanci kamar inganta kiwon lafiya, samar da tsaro, kallubalen ilimi da rage haraji.

A cewarsu, kirkirar sabbin masarautu a jihar zai haifar da barnar kudaden al'umma ne.

Hakan ya sa suke kira ga fadar shugaban kasa da sauran masu ruwa da tsaki su hana gwamnan kirkiran sabbin masarautun hudu domin kare mutunci da kimar al'addun jihar.

Al'umma da dama suna ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi a game da batun inda wasu ke goyon bayan kirkirar masarautun yayinda wasu kuma suke ganin hakan ba zai haifar da da mai ido ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel