Asarar haihuwa: Ta shigar da karar danta gaban kotu saboda barazanar halakata

Asarar haihuwa: Ta shigar da karar danta gaban kotu saboda barazanar halakata

Wata Mata mai suna Esther Edward ta shigar da karar danta mai shekaru 26, Godwin Edward gaban wata kotun majistri dake garin Yaba na jahar Legas bayan ya dauki alwashin halakata da wuka.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu ne aka tasa keyar Godwin zuwa gaban kotu, inda Dansanda mai shigar da kara, Sajan Modupe Olaluwoye yake tuhumarsa da laifin barazanar aikata kisan kai.

KU KARANTA: Jama’tu Nasril Islam ta koka ga Buhari game da tabarbarewar tsaro a Najeriya

Dansandan ya bayyana cewa Godwin wanda mazaunin unguwar Makoko na jahar Legas ya aikata wannan laifi ne a ranar 4 ga watan Mayu da misalin karfe 7 na yamma a gida mai lamba 3, layin Faloyi, unguwar Ishola dake yankin Yaba.

A daidai wannan lokacin ne Godwin ya dinga daga murya yana kiran babarsa ta fito ta kawo masa wukarsa data kwace daga hannunsa, idan kuma ba haka ba zai kwata da karfin tuwo, kuma sai ya yankata dashi idan ya kwace.

“Da kyar wasu mutane uku suka rirrikeshi a lokacin da yayi kokarin kai ma babarsa hari, kuma a wannan lokaci ne yake bayyana ma babar tasa cewa shi dan kungiyar asiri ne, kuma ya kashe mutane da dama da wannan wuka.” Inji Dansandan.

Dansandan ya kara da shaida ma kotun cewa laifin da ake tuhumar Godwin ya saba ma sashi na 56(a) na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Legas na shekarar 2015, kuma sashin ya tanadi hukuncin daurin shekara daya a gidan Yari.

Daga karshe bayan ta saurari dukkanin bangarorin dake shari’ar,Alkalin Kotun, mai sharia Oluwatoyin Oghere ta bada belin Godwin akan kudi N100,000, da kuma mutum guda daya da zai tsaya masa shima akan kudi N100,000, sa’annan ta dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Yuli.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel