Yadda na tsallake talalabiyar tsigewa daga kujerar shugaban majalisa na tsawon shekaru 8 - David Mark

Yadda na tsallake talalabiyar tsigewa daga kujerar shugaban majalisa na tsawon shekaru 8 - David Mark

- “Ba karfi na ba ne, yin Allah ne, da addu’o’in nagartattun ‘yan Najeriya da taimakon abokan aikina suka haifar da hakan.”

- "Mu mutunta junanmu kuma mu rika daukar shawarar da kowa zai ji ba a bar shi a baya ba.”

Tsohon shugaban majalisar dattijai Sanata David Mark, a ranar Larba ya bayyana yadda ya gudanar da mulkin majalisar na tsawon shekaru takwas ba tare da taka santsin talalabiya ba.

Sanator Mark yace “Ba karfi na ba ne, yin Allah ne, da addu’o’in nagartattun ‘yan Najeriya da taimakon abokan aikina suka haifar da hakan.”

Wannan yana kunshe ne a cikin wani bayanin da mataimakin Sanata Mark kan sha’anin watsa labarai, Paul Mumeh ya fitar.

Bayanin yace tsohon shugaban majalisar ya fada ma abokan siyasarsa da manyan shugabanni a kananan hukumomin Ado, da Oju da Obi dake jihar Benue, jiya a cigaba da ziyarar godiya da yake kaiwa zuwa kananan hukumomin mulki tara dake Benue ta kudu bayan shafe shekaru 20 a cikin majalisa..

“Ba ni da wani karfi. Albarkar Ubangiji ce, da goyon baya da addu’o’in mutanenmu da kyakkyawar fatar abokan aikina suka taimake ni na tsallake santsin talalabiyar tsigewa na tsawon shekaru takwas.”

KU KARANTA: Kafa Hukumar Bunkasa Arewa maso gabas: mayar da bukin ruwan kuri’un da aka yi man ne— Buhari

Mark yace kowa na iya samun cancantar yin shugabanci, “don haka mu mutunta junanmu kuma mu rika daukar shawarar da kowa zai ji ba a bar shi a baya ba.”

An ruwaito cewa Mark ya bayyana bukatar dawowa gida don gode wa mutanen shi kan gagarumin goyon bayan da suka ba shi, da karfafawa na tsawon shekaru 20.

Yace “meyiwuwa ban cimma dukkan buri na ba, amma na yi iyakar kokarina.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel