Rashin tsaro: Buhari na cikin ganawar sirri da shugabannin tsaro karo na 2 cikin sa’o’i 48

Rashin tsaro: Buhari na cikin ganawar sirri da shugabannin tsaro karo na 2 cikin sa’o’i 48

A yanzu haka Shugaban kasa Muhammadu Buhari na cikin ganawa da shugabannin tsaron kasar da na sauran hukumomin tsaro a fadar Shugaban kasa, Abuja.

An fara ganawar ne da misalin 11:30am a dakin taron shugaba Buhari da ke fadar Shugaban kasa.

Taron wanda ya kasance na biyu a cikin wannan makon, na zuwa ne bayan yawan fashi da sace-sacen mutane, da sauran matsalolin da tsaron kasar ke fuskanta.

Buhari a ranar Talata, 7 ga watan Mayu, ya samu jawabai daga shugabannin tsaro a fadar Shugaban kasa, Abuja.

Wadanda suka halarci taron sune Shugaban tsaro, Janar Gabriel Olonisakin, Shugaban soji, Laftanal janar Tukur Buratai; Shugaban sojin ruwa, Rear Admiral Ibok Ekwe Ibas da Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshall Abubakar Sadique.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An tsige kakakin majalisar Jigawa

Sauran sun hada da, mukaddashin sufeto janar na yan sanda, Mohammed Adamu, mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Babagana Monguno, ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, Ministan harkokin cikin gida, Janar Abdulrahaman Dambazau, Darakta Janar na hukumar liken asiri, Ahmed Abubakar, da Darakta Janar na yan sandan farin kaya, Yusuf Magaji Bichi.

Har ila yau, babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ma ya hallara a wajen ganawar tsaron.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel