Yanzu Yanzu: Buhari ya sake ba Emefiele mukami a karo na biyu

Yanzu Yanzu: Buhari ya sake ba Emefiele mukami a karo na biyu

Rahotanni sun kawo cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake zabar gwamnan babban bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele domin sake basa mukami a karo na biyu, jaridar Thisday ta ruwaito.

Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya fara nada Emefiele a 2014 sannan ya ci gaba a lokacin da Buhari ya hau mulki a 2015.

An tattaro cewa a safiyar ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu Shugaban kasar ya aika wata wasika ga Shugaban majalisar dattawa daidai da dokar babban bankin kasar inda a ciki yake bayyana sake zabar Shugaban babban bankin kasar a karo na biyu.

Yanzu Yanzu: Buhari ya sake ba Emefiele mukami a karo na biyu

Yanzu Yanzu: Buhari ya sake ba Emefiele mukami a karo na biyu
Source: Depositphotos

Bisa dokar CBN, sai majalisar dattawa ta tabbatar da nadin kafin ya fara aiki.

Wannan shine karo na farko tun 1999, lokacin da Najeriya ta dawo kan tafarkin damokreadiyya, da za a zabi wani ya shugabancin babban bankin kasar sau biyu.

Kafin ya fara aiki a matsayin gwamnan CBN, ma’aikacin bankin mai shekaru 57 ya kasance manajan darakta na bankin Zenith.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Buhari na cikin ganawar sirri da shugabannin tsaro karo na 2 cikin sa’o’i 48

A 2015 lokacin da faraqshin mai ya fara sauka a kasuwar duniya, anyi ta kira ga karya darajar naira. Amma Buhari yayi adawa da sawarar.

A matsayin gwamnan CBN, Emefiele ya gabatar da shirye-shirye da dama domin tabbatar da naira ta daidaita a matsayinta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel