Kafa Hukumar Bunkasa Arewa maso gabas: mayar da bukin ruwan kuri’un da aka yi man ne— Buhari

Kafa Hukumar Bunkasa Arewa maso gabas: mayar da bukin ruwan kuri’un da aka yi man ne— Buhari

Muhammadu Buhari jiya ya kaddamar da kwamitin gudanar da Hukumar Bunkasa Arewa maso Gabas (NEDC), wadda Manjo Janar Paul Tarfa mai ritaya ke jagoranta.

Hukumar ta NEDC nada alhakin sake gina Arewa maso gabas da ta’addancin kungiyar Boko Haram ta kacaccala.

A lokacin da a ake kaddamar da hukumar a dakin taron fadar shugaban kasa, kafin a fara gudanar da taron majalisar kasa da ake yi mako-mako, Shugaban kasar yace kafa hukumar godiya ce kan ruwan kuri’un da ya samu daga yankin a lokacin zaben 2015 da 2019.

A cewarsa hukumamar za ta rika nazari, da gudanarwa, da daidaitawa da kuma bada rahoton duk wani shirin tallafawar gwamnatin tarayya don kauce ma maimaitawar ayukka da barnar dukiya.

KU KARANTA: Karfin wutar lantarki ya ragu sanadiyyar matsalar da ta faru sau biyu cikin sa’o’i 18

“Dole ne ku rika hada kai da ma’aikatun gwamnatin tarayyar da abun ya shafa, da hukumomi da jihohi da kungiyoyin cigaba don aiwatar da dukkan shirye-shirye da manufofi da kuma yin aiki da kudaden da aka fitar don gudanar da shirin kamar yadda ya kamata.".

Ya kara da cewa kaddamar da hukumar NEDC cika alkawarin gwamnatinsa ne ga al’ummar mazabar yankin Arewa maso gabas a matsayin dabarun sake farfado da sha’anin tattalin arziki da zamantakewa na yankin bayan barnar da ‘yan ta’addar Boko Haram suka aikata da matsalar da ta’addanci yayi kan harkokin ilmi.

Shugaban kasa yace an kafa hukumar a karkashin dokar da ta bada damar kafa hukumar ta 2017 wadda aka sa ma hannu a ranar 25 ga watan Oktoba na 2017.

Don nuna sadaukarwar wannan gwamnatin ga fara aikinku, an samar da naira biliyan 10 a cikin kasafin kudin 2019. Ina sa ran za ku tabbatar da adalci wurin amfani da kudaden.”

Shugaban kasa ya umurci shugaban hukumar da yayi nazarin dukkan jihohin dake yankin don gano irin bukatun sake gina tattalin arziki da zamantakewa a yankin, saboda fitar da cikakken tsari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewarku tare da mu. Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Source: Hausa.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel