Buhari ya bukaci kotu ta yi watsi da sauraron karar Atiku

Buhari ya bukaci kotu ta yi watsi da sauraron karar Atiku

- Shugaban kasar ya tambayi kotu da ta fara duba manufarshi ta neman korar karar da jam'iyyar PDP ta shigar kotu akan magudin zabe

- Bukatar shugaba Buhari ta biyo bayan karar da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya shigar kotu da ke nuni da cewa jam'iyyar APC ta murde zaben da ya lashe na shugaban kasa ta bai wa shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi kotun daukaka karar da take sauraron karar zaben shugaban kasa, wacce dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya shigar, akan cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da hadin bakin jam'iyyar APC da hukumomin tsaro na kasar nan sun murde zaben da ya lashe sun bai wa shugaba Buhari.

Buhari ya bukaci kotu ta yi watsi da sauraron karar Atiku

Buhari ya bukaci kotu ta yi watsi da sauraron karar Atiku
Source: Depositphotos

Lauyan shugaba Buhari, Wole Olanipekun (SAN), ya ce shugaba Buhari ya aika da takardar bukatar ta shi ne a ranar 16 ga watan Afrilu.

A cikin takardar da shugaba Buharin ya rubuta, ya bukaci kotu ta yi watsi da sauraron karar Atiku, saboda bashi da takardun da ya kamata ace ya zama shugaban kasar Najeriya kamar yadda dokar kasa ta tsara.

KU KARANTA: Ashe jami'an 'yan sandan dake jihar Lagos kasuwanci suke zuwa yi ba aiki ba

A bayanin da ta yi, alkalin kotun daukaka karar, Mai Shari'a Zainab Bulkachuwa ta bayyana cewa maganganun jama'a su za su yanke hukunci akan karar da take sauraro.

Bayan haka kuma majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton cewa Peter Obi, wanda ya fito a matsayin mataimakin Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, ya halarci kotun sauraron karar wacce aka zauna jiya Laraba 8 ga watan Mayu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel