‘Dan takarar Jam’iyyar APC ne ya lashe zaben Jihar Osun – Inji Kotu

‘Dan takarar Jam’iyyar APC ne ya lashe zaben Jihar Osun – Inji Kotu

Kotun daukaka kara yayi zaman karshe yau a game da zaben gwamna da aka yi a jihar Osun kwanakin baya. Alkalan kotun sun bada hukuncin cewa jam’iyyar APC ce ta lashe zaben gwamna a Osun.

A zaman da kotun daukaka kara tayi a yau Alhamis, 9 ga Watan Mayun 2019, an yanke hukunci cewa jam’iyyar APC ce ta lashe zaben gwamna da aka yi a bara a Osun. Alkalan babban kotun sun yi watsi da hukuncin babban kotun tarayya.

Gwamna mai-ci Gboyega Oyetola ya shigar da kara gaban kotu inda yake kalubalantar nasarar da Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar adawa ta PDP ya samu a kotun sauraron karar zabe. Yanzu kotu ta ba Oyetola gaskiya a zaben jihar.

A zaman karshen da Alkalai 5 na kotun daukaka karar su kayi dazu nan, kotu ta rushe duk hukuncin da kotun da ke sauraron karar zabe yayi a Ranar 22 ga Watan Maris na bana. Alkali mai shari’a Jummai Sankey ce ta bada wannan hukunci.

KU KARANTA: Ana so Kotu rusa takarar PDP da APC a zaben Shugaban kasa

‘Dan takarar Jam’iyyar APC ne ya lashe zaben Jihar Osun – Inji Kotu
Kotu ta ba APC gaskiya bayan Gwamna Oyetola ya daukaka kara
Asali: Twitter

Daga cikin hujjojin da manyan Alkalai su ka bada shi ne, Alkali mai shari’a Peter Obiorah wanda yana cikin masu sauraron korafin zaben na jihar Osun, ba ya nan lokacin da aka rika zaman shari’a tsakanin PDP da APC amma aka sa sunansa.

Daga cikin hujjojin ‘dan takarar APC wanda shi ne gwamna a yanzu, shi ne Alkali Peter Obiorah bai yi na’am da sa hannun-sa da aka yi a hukuncin da aka gabatar a karamin kotun ba, don haka yace wannan shari’a sam ba za ta zauna ba.

Lauyan jam’iyyar APC a nasa bangare, shi ma ya soki hukuncin da Alkali Ibrahim Sirajo ya yanke bayan yayi la’akari da karashen zaben da aka yi a karshen Watan Satumba. Bayan an kai ga zagaye na biyu ne dai APC ta iya lashe wannan zaben.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel