Siyasar kabilanci ne ke lalata Najeriya – Inji Jega da Nnamani

Siyasar kabilanci ne ke lalata Najeriya – Inji Jega da Nnamani

Wani tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Ken Nnamani da tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega, a ranar Laraba, 8 ga watan Mayu sun bayyana cewa siyasar kabilanci ce ke kashe Najeriya.

Sunyi maganan ne a taron yaye dalibai da suka kammala karatu a jami’ar Nnamdi Azikiwe, Awka, a jihar Anambra, sun yarda cewa siyasar kabilanci ta kasance babbar abun da ya kawo tabarbare kasar.

Nnamani, yayin da yake gabatar da jawabi a taron, mai taken: "National Integration, Peace and Development,” yace yan siyasan Najeriya sun gaza daukar darasi daga kurakuren baya na siyasar kabilanci wanda yayi sanadiyan lalacewar kasar.

A cewar shi, jamhuriya ta farko ta kasa yin nasara saboda siyasar kabilanci.

Siyasar kabilanci ne ke lalata Najeriya – Inji Jega da Nnamani

Siyasar kabilanci ne ke lalata Najeriya – Inji Jega da Nnamani
Source: UGC

A cewar Jega, wanda ya kasance shugaba a taron, yace gazawar yan Najeriya wajen guje ma siyasar kabilanci ya kasance babbar matsalan da hadin kan kasa ke fuskanta.

A cewar shi, harkar siyasar Najeriya to koma hannun mutanen marasa kishin kasa.

KU KARANTA KUMA: Ra'ayoyin jama'a akan kacaccala masarautar kano zuwa yanka 5 da gwamnatin Ganduje tayi

Ya kara da cewa suna amfani da son zuciyan kabilanci wajen gudanar da shugabanci.

Yace lokaci yayi don fara bada gudumuwar ga cigaban siyasar kasar ba tare da barin kasar ba a hannun wadanda suka rasa alkibla da martaba ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel