Ra'ayoyin jama'a akan kacaccala masarautar kano zuwa yanka 5 da gwamnatin Ganduje tayi

Ra'ayoyin jama'a akan kacaccala masarautar kano zuwa yanka 5 da gwamnatin Ganduje tayi

Bayan saka hannu a kan wannan sabuwar dokar raba masarautar Kanoda gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje yayi, Al’umman Najeriya da dama sun je shafukan zumunta suna ta zayyana ra’ayoyinsu akan haka.

Mafi akasarin mutanen dai na adawa da nuna rashin jin dadi akan kacaccala masarautar mai tsohon tarihi da gwamnan yayi.

A ranar Laraba, 8 ga wata Mayu ne dai Ganduje ya rattaba hannu a kan sabuwar dokar kafa sabbin masarautu guda hudu (4) da suka hada da Rano, Karaye, Gaya da.

Ra'ayoyin jama'a akan kacaccala masarautar kano zuwa yanka 5 da gwamnatin Ganduje tayi

Ra'ayoyin jama'a akan kacaccala masarautar kano zuwa yanka 5 da gwamnatin Ganduje tayi
Source: UGC

Don haka mun leka shafinmu na Facebook inda muka zakulo maku wasu daga cikin ra’ayoyin mabiya shafin namu akan wannan lamari na rarraba masarautar Kano zuwa yanka biyar da gwamnati tayi.

Ga su kamar haka:

Wata mabiya shafin mai suna Hauwa Musa ta nuna ra’ayinta kamar haka: “Kayi ka gama daama ce, Amma zakayi nadama wlh,shi kuma sarki.wannan qaddara ce daga Allah, Allah yasa ta zame masa kaffara.”

Wani mai amani da shafin Facebook Sadeeq Muhammadu Lawal yace: “Gaskiya sai yau na kara yarda cewa Ganduje baya da Lisafi kokadan wannan kwama chala dakayi ba kanawa kayi mawa ba kadai arewa kataba amma sanni Sarasassaka baya hana gamji topo Gidan Govermen House gidan Haya ne gidan sarauta sai dan gado duk nisan jipa xata dawo kasa.”

Salisu Ango: “Allah yasa hakan ya zama alkhairi ga mutanen kano dama Najeriya gaba daya.”

Sai dai duk da hak lamarin yayi wa wasu dadi inda suke cewa:

Hafsat Rano: “Masha Allah muna godiya Allah yasaka maka da alherisa allahumma amen.”

KU KARANTA KUMA: Ba ka fi karfin doka ba – EFCC ta mayar da martani ga Saraki

Yahaya Galasco: “Allah yasanya alheri wannan shine cigaba ba a donkulle Abu a waje daya ba jigawa ma dabasu kai yawan kano ba sarakunan yanka guda 5 ne amma kano takare a 1 kamar idon babur wannan Abu yayi kyau Allah yakaroman cigaban kano Ameen ya Allah.”

Abban Siyama Kano: Alhamdulillahi baba ganduje.”

Umar Musa Abdullahi: “Wannan ganduje kayi dai dai domin anyi wannan tunanin tunlokacin marigayi allah yayimasa rahama gaskiyadai ganduje yacika mai kishin jahar kano.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel