Sabuwar majalisar Buhari: Yan damfara na gab da damfarar manyan jami’an gwamnati, DSS tayi gargadi

Sabuwar majalisar Buhari: Yan damfara na gab da damfarar manyan jami’an gwamnati, DSS tayi gargadi

Yayinda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yunkurin kafa sabuwar majalisa da za su gudanar da al’amuran kasar ta haanyar nade-naden wasu sabbin yan Najeriya da za sum aye gurbin wasu ministoci msu ci, sashin yan sandan farin kaya, ta yi gargadi akan yunkurin da wasu yan rufa ido ke yi domin damfarar makudan kudade daga manyan jami’an gwamnati.

Hukumar a wani jawabi dauke da sa hannun kakakinta, Peter Afunanya, a Abuja tace yunkurin da yan damfarar ke yi wani sabon hanya ne na damfara a kasar wanda aka shirya ta musamman akan manyan jami’an gwamnati.

Gargadin ya zo kamar haka: “Hukumar DSS na fatan jan hankalin jama’a, musamman shugabannin hukumomin gwamnati akan sabon hanyar damfara a kasar wanda aka shirya musamman a kansu.

“Bincike ya nuna cewa yan damfaran na amfani da sunan wasu manyan jagororin hukumomi wajen damfarar makudan kudade.

Sabuwar majalisar Buhari: Yan damfara na gab da damfarar manyan jami’an gwamnati, DSS tayi gargadi

Sabuwar majalisar Buhari: Yan damfara na gab da damfarar manyan jami’an gwamnati, DSS tayi gargadi
Source: UGC

“Wadannan yan damfaran na aiki ne a madadin manyan gwamnati, sannan su damfari mutum manyan kadarori da kudade.

“Abun zai cika da mutanen da ke neman sabbin mukamai ko sabonta wa’adin mukaminsu. Ana ganin za a ci kasuwar wannan muggun aiki a yanzu da mutane ke zawarcin mukaman gwamnati.

“Wannan jawaabin gargadi ne ga mutane domin su guje ma fadawa halaka."

KU KARANTA KUMA: Buhari ya shiga taro da manyan Gwamnati tun safe har cikin dare

Hukumar ta kuma bukaci mutane da su sanar da ita cikin gaggawa da zaran su ga wani abu da yayi kama da na yan damfara.

Ta kuma sha alwashin hada kai da sauran hukumomin tsaro domin kama yan damfara don tabbatar da kare mutunci da martabar tsaron kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel