Shirun Buhari na damun mu, inji yan majalisar dokokin APC

Shirun Buhari na damun mu, inji yan majalisar dokokin APC

-Yan majalisar dokokin APC na tsoron sake aukuwar abinda ya faru 2015 a zaben jagororin majalisa ta 9

-Wannan shirun da Buhari keyi ba shi bane mafi dacewa a yanzu, inji yan majalisar APC

Gabanin zaben sabbin shugabannin majalisar dokoki ta 9 wanda za’ayi cikin watan Yuni, zababbun yan majalisar dake karkashin jam’iyar APC sun nuna damuwar akan rashin tankawar Buhari bisa lamuran sabbin jagororin majalisar.

Wasu daga cikin yan majalisar da suka samu zantawa da jaridar Daily Independence, cewa sukayi "duba ga abinda ya faru a 2015 wanda baiyi mana dadi ba munyi tunanin shugaban kasa zai tattauna da dukkanin yan takarar kan cewa dole su mutunta dokokin jam’iyarmu."

Shirun Buhari na damun mu, inji yan majalisar dokokin APC

Shirun Buhari na damun mu, inji yan majalisar dokokin APC
Source: UGC

KU KARANTA:Kudin da aka sace a FIRS ba dukiyar harajin Talakawa bane – Fowler

Yayinda jam’iyar APC ta marawa sanata Ahmad Lawan baya domin kasancewa shugaban majalisar dattawa, akwai sanata Ali Ndume da sanata Danjuma Goje wadanda suka nuna takararsu a fili.

A tsarin karba-karba da jam’iyar APC ke amfani dashi, kakakin majalisa a wannan lokaci zai fito ne daga kudu maso yamma. Sai dai har ila yau wasu yan arewa daga cikin majalisar na nuna rashin amincewarsu da wannan tsari.

A daidai lokacinda Goje ke jiran magana daga bakin shugaban kasa kafin ya janye ko kuma ya cigaba da takarar, shi kuma Ali Ndume cewa yayi babu wanda ya same shi da maganar janye takara.

Da yake zantawa da yan jarida a Legas, sanata Ali Ndume yace jam’iyar APC bat ace masa kada ya tsaya takara ba. Inda ya kara da cewa kafin tsayawarsa takarar ya samu ganawa da wasu jiga-jigan jam’iyar APC babu kuma wanda y ace masa ya janye.

Hatta shugaban jam’iyar APC Adams Oshiomole cewa yayi sanata Ahmad Lawan shine dan takarar da jam’iyar APC ke marawa baya amma ba wai suna kokarin tilastawa sanatoci bane zabensa dole.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel