Ba ka fi karfin doka ba – EFCC ta mayar da martani ga Saraki

Ba ka fi karfin doka ba – EFCC ta mayar da martani ga Saraki

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa EFCC), a jiya Laraba, 8 ga watan Mayu tace Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki bai fi karfin doka ko bincike daga hukumar yaki da rashawar ba.

A wani jawabi daga mukaddashin kakakin EFCC, Tony Orilade yace tsohon gwamnan na jihar Kwara kuma Shugaban majalisar dattawa baya bukatar ya damu idan har ya san cewa bai da guntun kasha a tsuliyarsa.

Yace EFCC ta kula da martanin Saraki ga binciken hukumar game da albashinsa a matsayin gwamnan jihar Kwara da kuma yawan kudinsa a majalisar dattawa.

Saraki a ranar Talata a wani jawabi daga kakakinsa, Yusuph Olaniyonu ya bukaci EFCC da ta daina mayyar farauta akansa.

Ba ka fi karfin doka ba – EFCC ta mayar da martani ga Saraki

Ba ka fi karfin doka ba – EFCC ta mayar da martani ga Saraki
Source: Depositphotos

Saraki na martani ne ga wasikar EFCC ga gwamnatin jihar Kwara da ke neman bayanan albashi, alawus da duk wani kudi da Shugaban majalisar dattawa ya amfana a lokacin mulkinsa a matsayin gwamnan jihar Kwara tsakanin 2003 da 2011.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisa: Buhari ba zai hana ni takara ba - Ndume

Orilade a jiya Laraba yace jawabin Saraki, wannan ya nuna yana da dammar nuna ra’ayinsa akan lamarin, hukumar tace bata da niyan yiwa Saraki bita da kulli.

Orilade yace Saraki ya san cewa tushen binciken EFCC a yanzu zai bibiyi shekarun baya da dama.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel