Majalisar zartarwa ta tarayya ta ware N970.2m domin gina barikin hukumar kwastam

Majalisar zartarwa ta tarayya ta ware N970.2m domin gina barikin hukumar kwastam

-Gwamnatin tarayya zata ginawa hukumar kwastam gidaje kan N970.2m

-Kari akan gidajen, majalisar zartarwa ta aminta da siyo na'urorin sadarwa domin hukumar ta kwastam kan kudi N247.9m

Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ranar Laraba ta ware kudi N970.2m domin ginin didaje ga hukumar kwastam ta Najeriya.

Ministar kudi, Zainab Ahmad ce ta bayyana wannan zance bayan an kammala ganawar majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa wacce Buhari ya jagoranta, rahoto daga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN).

Majalisar zartarwa ta tarayya ta ware N970.2m domin gina bariki ga hukumar kwastam

Majalisar zartarwa ta tarayya ta ware N970.2m domin gina bariki ga hukumar kwastam
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Kudin da aka sace a FIRS ba dukiyar harajin Talakawa bane – Fowler

An dau tsawon lokaci ana wannan ganawa wacce ta kai har dare. Zainab tace ginawa jami’an hukumar kwastam gidaje nada matukar muhimmacin domin aikinsu zai fi kyau idan suna zauna wuri guda a bariki.

“ A yau hukumar kwastam ta samu yarjewa akan ginin gidajen jami’anta. Abinda kuma hukumar zata mallaka yanzu shine gidaje 42 wanda kudinsu ya kama N152m ga ko wane sashen daga cikin sassa 6.

“ Amincewar da muka samu yau jimillar N970.2m tare dad a kudin VAT a ciki. A burin da hukumar ta kwastam na kasancewa hukumar da zata iya gogayya da sauran kasashen duniya, ta samu amincewar gwamnatin wurin sayen kayayyakin sadarwa na zamani.” Zancen Zainab Ahmad.

Ministar tace sayen wadannan na’urorin sadarwa ya zama dole domin bunkasa aikin hukumar kwastam, ta hanyar hakan zasu magance matsalaloli fasa kori da shigowa da haramtattun kaya da wasu mutane keyi.

“ An bayar da wannan kwantaragin ne kan kudi N247.907m kuma za’a kawo wadannan na’urorin cikin makonni 8.” A fadar Zainab.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel