Shugabancin majalisa: Buhari ba zai hana ni takara ba - Ndume

Shugabancin majalisa: Buhari ba zai hana ni takara ba - Ndume

Daya daga cikin masu takarar kujerar shugabancin majalisar dattawa, Sanata Mohammed Ali Ndume ya ce ya yi imanin shuguban kasa Muhammadu Buhari ba zai umurci shi ya janye takararsa ba.

Ndume ya ce shugaban kasan mutum ne mai mutunta demokradiya saboda hakan ba zai yi katsalandan ba a cikin zaben shugabanin majalisar na tarayya.

A ganawar da ya yi da wakilan Daily Trust a ranar Laraba a Abuja, Ndume ya kuma ce baya bukatar wani daga cikin masu takarar shugabancin majalisar ya janye masa.

Shugabancin majalisa: Buhari ba zai hana ni takara ba - Ndume

Shugabancin majalisa: Buhari ba zai hana ni takara ba - Ndume
Source: UGC

DUBA WANNAN: Jonathan ya ci amanar PDP a zaben 2019 - Kungiya

"Majalisa zaure ne na dattawa saboda haka bana tsamanin suna bukatar wani ya zaba musu shugaba, a kyalle su suyi zabensu ba tare da katsalandan ba," a cewar Ndume.

Ya cigaba da cewa, "Bana tunanin shugaban kasa zai bukaci in janye takara ta saboda bai taba yin katsalandan a harkokin zabe ba. Hasali ma, ban ga dalilin da zai sa in janye ba.

"A bari muyi zabe sanatocin su zabi wanda suke so. Bana goyon bayan tilastawa jama'a shugabanni. Ba a tilastawa mutane zaben shugaban kasa ba, shima shugaban jam'iyya na kasa ba tilas yasa aka zabe shi ba. Bana tunanin wani zai tunkare ni a kan batun janye takara.

"A lokacin da shugaban kasa ya yi takara karo na farko, mutane kamar su Kwankwaso, Okorocha, Sam Nda-Isiah da sauransu duk sunyi takarar. Okorocha ya yi takarar duk da cewa arewa aka mika wa kujerar a wannan lokacin.

"Maganan gaskiya ita ce bana son kowa ya janye min. Lokacin zaben cikin gida, jam'iyyar tayi yunkurin cire sunayen wasu 'yan takara amma na ce bana son ayi hakan. Abinda kawai za mu iya yi shine mu zauna tsakaninmu mu tsayar da wanda muke so," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel