Kudin da aka sace a FIRS ba dukiyar harajin Talakawa bane – Fowler

Kudin da aka sace a FIRS ba dukiyar harajin Talakawa bane – Fowler

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, ta soma gudanar da wani bincike na musamman a game da wasu kudi da aka wuwara daga asusun hukumar FIRS.

Kamar yadda mu ka samu labari, shugaban hukumar FIRS mai tara kudin-shiga a Najeriya. Mista Babatunde Fowler, ya tabbatarwa manema labarai cewa babu shakka wasu kudi sun bace daga hukumar a cikin ‘yan kwanakin nan.

Babatunde Fowler yake cewa wasu ma’aikata sun yi sama-da-fadi da alawus din da ake warewa wadanda su kayi tafiya watau DTA. Wasu ma’aikatan hukumar sun karbi kudin zirga-zirga da nufin za su yi tafiya, amma ba su yi ba.

Fowler yake cewa wasu kuma sun amsa alawus din nan DTA ba tare da sun cika yawan kwanakin da su kace za su yi ba. Wannan ya sa aka gayyaci hukumar EFCC ta binciki wannan lamari domin hukunta duk wanda aka kama da laifi.

KU KARANTA: Wani mai zaman kashe-wando yayi abin da ya kai shi kurkuku

Kudin da aka sace a FIRS ba dukiyar harajin Talakawa bane – Fowler

Tunder Fowler yace Ma'aikatansa sun wawuri wasu alawus
Source: Depositphotos

Shugaban na FIRS yana ganin cewa binciken da wani zai zo daga waje ya gabatar a cikin hukumar ta FIRS zai fi inganci a kan manyan ma’aikatan hukumar su binciki duk wadanda ake zargi. Fowler yace wannan zai taimakawa hukumar.

Har wa yau, Mista Fowler yake cewa wadannan kudi da wasu ma’aikatansa su ka wawura, ba ya daga cikin harajin Bayin Allah da su ke karba a Najeriya. Fowler yace harajin da FIRS ta ke tarawa gwamnati yana cikin asusun CBN na Najeriya.

A karshe, shugaban na FIRS ya bayyana cewa hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da EFCC da kuma jami'an DSS su na da hurumin da za su shiga cikin duk wata ma’aikata domin yin bincike muddin aka ji cewa alamun ana yin ba dai-dai ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel