Dalibi ya yi ma Farfesa yankan rago bayan cacar baki ya kaure a tsakaninsu

Dalibi ya yi ma Farfesa yankan rago bayan cacar baki ya kaure a tsakaninsu

Wani dalibin Ilimi ya hau dokin zuciya inda ya kashe Malamarsa, kuma Farfesar ilimi a jami’a bayan wata zazzafar cacar baki ta kaure a tsakaninsu game da aikin binciken da yake gudanawarwa na kammala karatun digiri na farko.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya auku ne a wata ranar Litinin cikin shekarar 2016 a jami’ar Arewacin Sumatra Muhammadiyah dake kasar Indonesia, inda Farfesa HJ Nurain Lubis yar shekara 57 take koyarwa a tsangayar Ilimi.

KU KARANTA: Jama’tu Nasril Islam ta koka ga Buhari game da tabarbarewar tsaro a Najeriya

Dalibi ya yi ma Farfesa yankan rago bayan cacar baki ya kaure a tsakaninsu

Malama Lubis
Source: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa dalibin mai suna Romardo Sah Siregar mai shekari 21 ya aikata wannan aika aika ne a lokacin da suke tattaunawa da Farfesa Lubis game da aikin binciken da take duba masa, daga nan ne musu ya kaure a tsakaninsu har ta kai ga yayi mata yankan rago.

Majiyarmu ta kara da cewa Sah ya aikata ma Farfesa Lubis wannan danyen aiki ne a daidai lokacin da tafito daga bayan gida, sa’annan shima nan da nan ya shige cikin bayin da nufin boyewa, duk da cewa an garzaya da Lubis asibiti, amma bata sha ba.

Da kyar da sudin goshi jami’an Yansanda suka ceci Siregar sakamakon fusatattun matasa sun kewaye bayin gidan suna tsimayin fitowarsa domin su kasheshi shima, a yanzu dai Yansanda sun kaddamar da bincike akansa yayin da yake fuskantar tuhumar kisan kai.

A sakamakon haka saida hukumar gudanarwar jami’ar ta sanar da rufe jami’ar na tsawon kwanakin biyu domin yin jimamin mutuwar Farfesa HJ Nurain Lubis, kamar yadda daraktan harkar ilimi na jami’ar ya bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel