Buhari ya shiga taro da manyan Gwamnati tun safe har cikin dare

Buhari ya shiga taro da manyan Gwamnati tun safe har cikin dare

A duk mako a kan yi taron majalisar zartarwa na FEC inda Ministoci da kuma wasu manyan mukarraban shugaban kasa da kusoshin gwamnatin tarayya su ke zama su tattaunawa sha’anin kasa.

A wannan makon, mun samu labari cewa zaman na FEC ya kai har an yi dare a dalilin yawan batutuwan da Ministocin ke tattaunawa a kai da shugaban kasar. An dai kai har can cikin dare ana yin wannan taro a fadar shugaban kasa.

Manema labarai sun rahoto mana cewa an fara taron na jiya Laraba 8 ga Watan Mayu ne tun karfe 11:00 na safe, amma an haura karfe 9:30 na dare ana yin wannan taro kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana a cikin daren yau.

An shiga wannan babban taro ne da nufin tattaunawa a kan wasu takardu 25 da Ministocin kasar su ka kawowa gaban teburin shugaban kasa. Sai dai kamar wasa, sai da wannan zama ya kai aka shafe kusan sa’a 11 ana ta faman tattaunawa.

KU KARANTA: Binciken Uzodinma ya raba kan Minista da Hadimin Buhari

Buhari ya shiga taro da manyan Gwamnati tun safe har cikin dare

Gwamnatin Buhari ta kafa tarihin jagorantar wani dogon zaman FEC
Source: Facebook

Kamar yadda mu ka samu labari, an je hutu har sau 2 yayin da ake cikin taron domin bukatar ibada. Ana cikin taron ne ma dai aka samu sarari domin Musulmai da ke azumi a cikin wurin taron su samu zuwa su sha ruwa su koma bakin aiki.

Hakan na zuwa ne dai a daidai lokacin da wa’adin wannan gwamnati ke shudewa inda har shugaban kasa ya fadawa Ministocinsa su fara shirin barin ofishohin su. Tun daga 2015 dai ba a taba yin dogon zaman FEC irin na na makon yau ba.

Kafin a shiga wannan taro, shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da majalisar da za ta rika lura da sa ido a hukumar NEDC da aka kafa mai kula da sha’anin Arewa maso Gabas da yakin Boko Haram ya ci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel