Zaratan Sojojin Najeriya sun halaka yan bindiga a wani harin tsakar dare a Kaduna

Zaratan Sojojin Najeriya sun halaka yan bindiga a wani harin tsakar dare a Kaduna

Biyo bayan tsegumin bayanan sirri da wani matashi dan kishin kasa ya labarta ma rundunar Sojan kasa game da shirin kai hare hare da wasu gungun yan bindiga ke shiryawa, rundunar ta aika da dakarunta, inda suka tafka ma yan bindigan asara ruwa uku da goma.

Legit.ng ta ruwaito da misalin karfe 4:30 na daren Larab, 8 ga watan Mayu ne dakarun rundunar Sojan kasa suka far ma yan bindigan a mabuyarsu dake wani gidan gona inda suke sakaya mutanen da suka yi garkuwa dasu.

KU KARANTA: Ka fuskanci matsalar tsaro a Kaduna ka rabu da shuwagabannin mu – Yarbawa ga El-Rufai

Zaratan Sojojin Najeriya sun halaka yan bindiga a wani harin tsakar dare a Kaduna

Zaratan Sojojin Najeriya sun halaka yan bindiga
Source: UGC

Shidai wannan gidan gona mai suna Gonan Bature yana kusa da gonar Kasarami ne dake cikin karamar hukumar Chikun ta jahar Kaduna, kuma an rufe gonar ne sakamakon ayyukan yan bindigan, wanda hakan ya basu damar mayar dashi sansaninsu.

A yayin wannan samame da Sojoji suka kai, sun samu nasarar halaka yan bindiga biyu, tare da kwato makaman da suka hada da AK 47 guda 2, alburusai da dama da kuma wayoyin salula kirar Techno guda biyu.

Zaratan Sojojin Najeriya sun halaka yan bindiga a wani harin tsakar dare a Kaduna

Zaratan Sojojin Najeriya sun halaka yan bindiga
Source: UGC

Kaakakin rundunar Sojan kasa, Kanal Sagir Musa ne ya sanar da wannan nasara da Sojoji suka samu, sa’annan ya bada tabbacin a shirye rundunar take don kare rayuka da dukiyoyin al’umman Najeriya gaba daya.

Daga karshe Sagir ya jinjina ma matashin daya kai ma Sojojin tsegumi akan yan bindiga, sa’annan ya kara jaddada bukatar samun makamancin wannan rahoto daga bakunan jama’an gari don taimaka musu wajen yaki da yan bindiga, yan ta’adda da kuma masu garkuwa da mutane.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel