An nada Umar Gonto a matsayin shugaban hukumar FHA

An nada Umar Gonto a matsayin shugaban hukumar FHA

Umar Gonto, gogaggen masanin ilimin shari'a, ya zama sabon babban darektan gudanar wa na hukumar gidajen gwamnatin tarayya (FHA).

Nadin Gonto ya biyo bayan karewar zangon shugaban hukumar FHA, Mohammed Al-Amin, a ranar 6 ga watan Mayu.

Wani jami'i a ma'aikatar aiyuka, gidaje da lantarki da ya nemi a boye sunan sa, ya ce an bi dokokin tsarin mulkin Najeriya da na aikin gwamnati wajen nadin Gonto. Ya ce Gonto ya zama shugaba ne kasancewar shine babban jami'i a hukumar bayan karewar zangon Al-Amin.

An nada Umar Gonto a matsayin shugaban hukumar FHA

Umar Gonto
Source: Twitter

Kafin nadin shi, Umar na rike da mukamin manaja mai kula da bangaren shari'a a hukumar FHA.

DUBA WANNAN: Kisa da kona gidaje: Hotunan barnar da mayakan Boko Haram suka tafka a Molai

Gonto ya yi karatu a sashen ilimin shari'a na jami'ar Maiduguri, ya kammala karatun sa a shekarar 1986.

Mamba ne a kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) da kuma kungiyar lauyoyi ta kasa da kasa (IBA).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel