Jihar Kuros-Riba za sa ta dorawa Buhari ciwon-kai wajen zaben Minista

Jihar Kuros-Riba za sa ta dorawa Buhari ciwon-kai wajen zaben Minista

Yayin da shugaba Muhammadu Buhari yake shirin kafa sababbin Ministoci da sauran kusoshin gwamnati a mulkin sa na biyu, mun fahimci cewa masu neman mukamai a gwamnatin nan su na kara yawa.

Akalla ba a kasara ba, mutum 15 su ke neman su dace da kujerar Minista a jihar Kuros-Riba a cikin gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Jaridar Vanguard tace ‘yan siyasa da dama su na sa ran samun Minista a kasar.

Da-dama daga cikin ‘yan takarar jam’iyyar APC da su ka fito zabe a Yankin kudancin Najeriya sun sha kasa ne a hannun PDP. Wannan ya sa da yawa daga cikin ‘yan takaran Kuros-Riba su ka dawo su na so a basu mukamin Minista a 2019.

APC ta sha kashi ne a yankin Kudu a dalilin karfin PDP da kuma rikicin-cikin gida na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya. Wannan ya sa wasu daga cikin manyan APC su ka fara magana a kan wadanda su ka dace su zama Ministoci daga Kudu.

KU KARANTA:

Jihar Kuros-Riba za sa ta dorawa Buhari ciwon-kai wajen zaben Minista

Manyan ‘Yan siyasan APC a Kuros Riba sun yi can a kan kujerun Ministoci
Source: Facebook

Wani Jigon APC a Kuros Riba, Utum Eteng yayi kira ga shugaban kasa Buhari da ya guji nada wadanda su ka kawo masa matsala a wajen zaben bana a kan kujerar Minista. Eteng ya nemi Buhari ya zakulo wadanda su ka san aiki wannan karo.

Eteng yana ganin cewa kwararru ya kamata Buhari ya tafi da su wadanda za su kashe dare da rana domin ganin cigaban gwamnatinsa. Babban Jagoran na APC ya kuma ce ayi watsi da duk wanda bai yi wa Buhari aiki a wajen zaben 2019 ba.

Ganin cewa kusan mutane 15 ke neman Minista daga Kuros-Riba, Cif Etum Eteng wanda yake da ra'ayin cewa akwai manyan APC da aka hada baki da su wajen ganin PDP tayi nasara a Yankin Kudu, ya fito yace a guji kafa gwamnati da ruwa-biyu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel