Binciken Hope Uzodinma ya raba kan Malami da Obono-Obla

Binciken Hope Uzodinma ya raba kan Malami da Obono-Obla

Ba da dadewa bane wani kotun tarayya da ke zama a Abuja ya ba Ministan shari’an Najeriya, Abubakar Malami SAN dama ya binciki ‘dan takarar gwamnan APC a jihar Imo a zaben da aka yi bana.

Alkali mai shari’a Okon Abang ya ba Abubakar Malami izinin ya binciki zargin da ke kan wayar Hope Uzodinma wanda ya rikewa jam’iyyar APC tuta a zaben jihar Imo. Ana zargin Uzodinma da kin bayyanawa hukukama dukiyarsa.

Kotu ta nemi Ministan shari’ar kasar ya karbe binciken da kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin karbo dukiyar gwamnati da ke hannun wasu manyan ma’aikata da 'yan siyasan kasar. Hadimin Buhari yake jagorantar wannan kwamiti.

Shugaban kwamitin na SPIPRP, Okoi Obono-Obla, bai ji dadin wannan mataki da kotu ta dauka ba, inda har Lauyan wannan kwamiti na SPIPRP ya dumfari kuliya yana mai so ayi watsi da damar da aka ba Ministan na karbe wannan binciken.

KU KARANTA: ‘Dan Majalisa ya na so a duba lamarin albashin Alkalan Najeriya

Binciken Hope Uzodinma ya raba kan Malami da Obono-Obla

Ana fada tsakanin Malami da Hadimin Buhari a kan Uzodinma
Source: Twitter

Obono-Obla ta bakin Lauyan na sa yake cewa Abubakar Malami bai da ikon da zai karbe wannan bincike ya dawo hannunsa, saboda ganin matakin da shari’ar ta ke ciki. Sai dai Kotu ta nunawa mai karar cewa Ministan yana da cikakken iko.

Alkali mai shari’a Abang, ya bada hukuncin cewa dokar kasa ta ba Ministan shari’a damar karbe duk wata shari’a a fadin kasar. Sashe na 174(1) ne ya ba Minista wannan dama a matsayin sa na shugaban mai gurfanar da masu laifi a Najeriya.

Alkali Abang ya fadawa wannan kwamiti na Obono-Obla da su yi wa AGF Abubakar Malami biyayya. Yanzu dai za a cigaba da binciken wannan Sanata da ya sha kasa a takarar gwamna a jihar Imo.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel