Yanzu-yanzu: Akwai yiwuwar tafiya yajin aiki a fadin Najeriya

Yanzu-yanzu: Akwai yiwuwar tafiya yajin aiki a fadin Najeriya

Bayan anyi kare jini biri jini tsakanin 'yan zanga-zanga da 'yan daba a Abuja, kungiyar kwadago ta kasa ta ce kowanne lokaci za ta iya sanya ma'aikatan Najeriya tafiya yajin aiki

Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi barazanar tafiya yajin aiki na kasa baki daya, bayan rikicin da ke tsakanin kungiyar ma'aikata ta kasa da kuma ministan ayyuka na kasa, Dr. Chris Ngige kan rashin amincewarsa akan zabin kungiyar ma'aikatan na Comrade Frank Kokori a matsayin shugaban hukumar inshora na kasa (NISTF).

Yanzu-yanzu: Akwai yiwuwar tafiya yajin aiki a fadin Najeriya
Yanzu-yanzu: Akwai yiwuwar tafiya yajin aiki a fadin Najeriya
Source: UGC

Idan kuna biye damu majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton yadda zanga-zangar kungiyar ma'aikatan ta juye ta zama wurin zubar da jini, yayin da wasu wanda ake zargin 'yan daba ne suka je wurin zanga-zangar suka dinga saran ma'aikatan masu zanga-zangar, hakan ya yi sanadiyyar jin munanan raunika ga da yawa daga cikin ma'aikatan.

KU KARANTA: 'Yan zanga-zangar da Atiku ya dauka sun afka cikin kotun da ake sauraron karar zabe

Za mu kawo muku cikakken rahoton halin da ake ciki nan ba da dadewa ba...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel