Wahalar da na sha a APC ya fi na PDP sau 10 – Okorocha

Wahalar da na sha a APC ya fi na PDP sau 10 – Okorocha

- Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, yace wahalar da ya sha a APC ya fi na PDP sau goma

- Okorocha wanda yace har yanzu shi dan APC ne ya caccaki shugabannin jam’iyyar mai mulki

- Ya yi danasanin barin PDP zuwa APC da yace suna kokarin kai shi kasa

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, yace jam’iyyar All Progressives Congress(APC) mai mulki ta muzguna masa fiye da muzgunawar da ya kamata da fuskanta a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) sau goma.

Okorocha, wanda yace har yazu shi dan APC ne duk da kora da halin da ake kokarin yi masa a jam’iyyar, ya caccaki Shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole da wasu shugabanni da ke aiki tare da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) don ganin cewa bai samu takardar shaidar cin zabensa ba a matsayin zababben sanatan yankin Imo ta gabas.

Wahalar da na sha a APC ya fi na PDP sau 10 – Okorocha

Wahalar da na sha a APC ya fi na PDP sau 10 – Okorocha
Source: Twitter

Yace yayi danasanin abunda ya sa shi barin PDP sannan ya bi sahun jam’iyya mai mulki da ke kokarin lalata masa kudirin siyasarsa.

KU KARANTA KUMA: Bayan 'sa hannun' Ganduje: Jerin kananan hukumomin dake karkashin masarautun Kano 5

Gwamnan ya yi Magana ne a wani taron tattaunawa da manema labarai a babbar birnin tarayya, Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel