2023: Ku manta da burin kujerar shugaban kasa, ku samar da aiki ga Matasan ku

2023: Ku manta da burin kujerar shugaban kasa, ku samar da aiki ga Matasan ku

Mista Johnpaul Anih, jagoran wata kungiyar Matasa ta Coal City Youth Initiative, ya nemi 'yan siyasar kabilar Ibo da su sassauta burace-buracen samun kujerar shugaban kasa a 2023. Ya ce a madadin haka su jajirce wajen samar da aiki ga Matasan su.

Jagoran kungiyar Coal City Youth Initiative, ya nemi 'yan siyasar kabilar Ibo da su daina hankoron samun kujerar shugabancin kasa a zaben 2023. Ya ce a madadin haka su yi tsayuwar daka ta samar da ayyukan yi ga Matasan su.

Buhari yayin da ya kaiwa al'ummar kabilar Ibo ziyara

Buhari yayin da ya kaiwa al'ummar kabilar Ibo ziyara
Source: UGC

Mista Anih ya yi hasashen cewa, samun kujerar shugabancin Najeriya ga 'yan kabilar Ibo a zaben 2023 lamari ne tamkar mafarki da ba zai taba kasancewa gaskiya ba duba da yadda tarihin kasar ya haskaka yadda jinin su ya zamto tamkar haramiya ga jagorancin kasar nan tun yayin dawowa bisa turba ta dimokuradiyya.

Yayin wata hira da manema labarai na jaridar Vanguard, Mista Anih ya ce aniyyar samun kujerar shugaban kasa a zaben 2023 da 'yan kabilar Ibo su ka kudirta a kwana-kwanan nan cikin birnin Enugu ba zai haifar da wani 'Da mai ido ba illa iyaka siyasa irin ta son zuciya da ta rufe idanun shugabannin yankin Kudu maso Gabashin kasar nan.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa za mu gudanar da bincike a kan Saraki - EFCC

Ya ce duba da yadda shimfidar tarihi ya zayyana, al'ummar kabilar sun gaza samar da shugaban kasa tun yayin da Najeriya ta dawo kan tsari na dimokuradiyya. Ya nemi shugabannin kabilar Ibo da su tumke damarar samar da ayyukan yi ga Matasan su domin dakile aukuwar miyagun laifuka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel