Jonathan ya yi watsi da jam'iyyar PDP a zaben 2019

Jonathan ya yi watsi da jam'iyyar PDP a zaben 2019

Rahotanni da ke zuwa mana a yanzu sun bayyana cewa, tsohon shugaban kasar Najeriya Dakta Goodluck Ebele Jonathan tare da mai dakin sa Patience Jonathan, sun juyawa jam'iyyar PDP baya a yayin babban zaben kasa na bana.

Wata kungiya ta Save Ogbia Movement SOM, ita ce ta bayar da shaidar hakan tare da jaddada cewa tsohon shugaban kasar Najeriya tare da mai dakin sa sun yi watsi da jam'iyyar su ta PDP a yayin babban zaben kasa na 2019.

Jonathan ya yi watsi da jam'iyyar PDP a zaben 2019

Jonathan ya yi watsi da jam'iyyar PDP a zaben 2019
Source: UGC

Kungiyar SOM cikin babatu ta bayyana yadda tsohon shugaban kasa ya ci moriyar ganga kuma ya yada kauranta yayin da ya yi watsi da goyon bayan dukkanin 'yan takara na jam'iiyyar sa ta PDP musamman a yankin karamar hukumar Ogbia da kuma ilahirin shiyyar Bayelsa ta Gabas.

Kamar yadda jaridar The Nation ta hikaito wannan rahoto, kungiyar ta fidda sanarwar hakan da sanadin sakataren ta, Franklin Azibola James yayin ganawar sa da manema labarai a ranar Laraba cikin birnin Yenagoa.

Mista Franklin ya bayyana rashin jin dadin dangane da yadda tsohon shugaban kasa ya gaza bayar da wata muhimmiyar gudunmuwa ga jam'iyyar sa ta PDP da hakan ya haifar ma ta da shan mugunyar kaye mazabar sa ta Gabashin jihar Bayelsa.

KARANTA KUMA: Kungiyar Makafi ta mika bukatar neman aiki a gwamnatin tarayya

Sai dai ko shakka ba bu kungiyar na da cikakken yakinin yadda tsohon shugaban kasa ya hada gangami a farfajiyar gidan sa da ke garin Otuoke domin jaddadawa magoya bayan sa zaben dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Kungiyar SOM ta ce rawar ta Jonathan ya taka wajen watsi da jam'iyyar PDP ta yi tasirin gaske sakamakon yadda ta haifar da rashin jituwa da kuma kalubalai na koma baya a mahaifar sa da ta kasance jihar Bayelsa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel