Kungiyar Makafi ta mika bukatar neman aiki a gwamnatin tarayya

Kungiyar Makafi ta mika bukatar neman aiki a gwamnatin tarayya

Kungiyar Makafi ta Najeriya, ta mika muhimmiyar bukatar neman aiki samun aiki ga mambobin ta a ma'aikatu na gwamnatin tarayya. Kungiya ta yi wannan kira yayin wata hira da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na kasa a jihar Legas.

A ranar Laraba, 8 ga watan Mayun 2019, jagoran kungiyar Makafi na Najeriya, Malam Isiyaku Adamu, ya nemi hukumar ma'aikatun gwamnatin tarayya da ta kebance wadatattun guraben aiki ga mambobin yayin daukar ma'aikata.

Kungiyar Makafi ta mika bukatar neman aiki a gwamnatin tarayya
Kungiyar Makafi ta mika bukatar neman aiki a gwamnatin tarayya
Source: UGC

A yayin da Makafi ba su da alaka da guraben aiki a hukumomin tsaro da ke fadin kasar nan, kungiyar makafai ta nemi gwamnatin tarayya ta rika kebance wadatattun gurabe yayin daukar ma'aikata a sauran ma'aikatu da cibiyoyin gwamnati a kasar nan.

Malam Isiyaku ya ce a yayin da makafi da sauran nakasassu ke samun horaswa iri guda da masu cikakkiyar lafiya tun daga matakin karatu na firamare har zuwa matakin kammala karatu a jami'o'i, akwai bukatar a daidaita su ta fuskar adalci kamar sauran al'umma wajen bayar da aiki.

Ya ci gaba da cewa, muddin nakasassu za su samu shiga ta fuskar samun aiki a ma'aikatu cikin fadin kasar, hakan zai yi tasiri wajen kwadaitar da manyan gobe wajen gasar neman ilimi domin samun kyakkyawar makoma.

KARANTA KUMA: Garkuwa da Mutane: Likitoci sun kauracewa aiki a jihar Kuros Riba

Da ya ke ci gaba da mika kokon bara ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugaban kungiyar na makafi ya kuma kara da cewa, da yawa daga cikin masu nakasa ta makanta ba su da aikin yi a mafiya akasarin sassan kasar nan da hakan ya yi sanadiyar yawaitar masu barace-barace a kan hanyoyi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel