Jonathan ya ci amanar PDP a zaben 2019 - Kungiya

Jonathan ya ci amanar PDP a zaben 2019 - Kungiya

Kungiyar Save Ogbia Movement (SOM) ta ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da uwargidansa Patience sun ci amanar jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) a babban zaben kasa na 2019.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ya ce tsohon shugaban kasar ya amfana da PDP sosai amma daga baya ya yi watsi da 'yan takarar jam'iyyar musamman a karamar Ogbia da kuma mazabun Gabashin jihar Bayelsa.

Sanarwar mai dauke da sannun sakataren kungiyar, Franklin Azibola James ta ce tsohon shugaban kasan ya kira taron magoya bayansa a Otuoke daf da zabe inda ya ce musu su zabi dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar amma suna iya zaban duk wanda suke so a zabukan 'yan majalisun tarayya.

Jonathan ya ci amanar PDP a zaben 2019 - Kungiya

Jonathan ya ci amanar PDP a zaben 2019 - Kungiya
Source: UGC

DUBA WANNAN: Kirkirar sabbin masarautu: Mutanen Kano ba za su lamunta ba - Naniya

James ya koka kan yadda tsohon shugaban kasan ya yi watsi da 'yan jam'iyyar wanda hakan ya jefa su cikin mawuyacin hali har ta kai ga jam'iyyar adawa ta lashe zaben sanata a mazabar sa.

Ya kuma ce tsohon shugaban kasa Jonathan ya gaza hada kan 'yan jam'iyyar PDP na jiharsa a lokacin da ya ke kan karagar mulki sai dai ya bari hadimansa suka dinga raba kawunnan 'yan jam'iyya.

Ya ce: "Tsohon shugaban kasan ya cigaba da gina kansa ne a maimakon daukan matakan da za su bunkasa jam'iyyar PDP. Duk abinda ya samu a yau, jam'iyyar PDP ce sanadi.

"Tun daga asalinsa na talaka ya zama mataimakin gwamna, sannan ya zaman gwamna kuma ya zama mataimakin shugaban kasa daga karshe ya zama shugaban kasa. Abin mamaki ne mutumin da ya samu irin wannan gatan zai juya ya ci amanar jam'iyyar da ta bashi damar zama shugaban kasa.

"Babban zaben kasa da ta gabata abin misali ne, tsohon shugaban kasar mu ya yiwa jam'iyyar ADC aiki. Ba za mu cigaba da yin rufa-rufa ba. Ba zamu cigaba da yin shiru a kan cin amanar da Jonathan ya yiwa PDP a jiharsa ba.

"Duk wanda ya ziyarci Ogbia ba zai yarda wai mun taba samun shugaban kada daga garin mu ba. Ya gaza kammala titin Kudu - Yamma. Ya gaza gina titi a karamar hukumar mu ta Ogbia."

James ya shawarci tsohon shugaban kasar ya ajiye son kai ya yi aiki tare da shugabanin jam'iyyar PDP domin nuna godiya bisa karamcin da aka yi masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel