Dan majalisar dattawa ya nemi a kara yawan tarago kan layin Abuja zuwa Kaduna

Dan majalisar dattawa ya nemi a kara yawan tarago kan layin Abuja zuwa Kaduna

-Sanata Ali Ndume ya nemi gwamnatin tarayya ta kara jiragen kasa kan layin dogo dake tsakanin Kaduna zuwa Abuja

-Wannan kiran ya biyo bayan tsayuwa tun daga Abuja har Kaduna da sanatan yayi cikin jirgin inda baya fatan sake aukuwar hakan

Sanata Ali Ndume dan majalisar dattawa daga jihar Borno ya nemi gwamnatin tarayya da ta kara yawan tarago kan layin dogo na Abuja zuwa Kaduna.

Sanatan yace karin taragon zai kawo ma matafiya sauki. Yayi wannan kiran ne ranar Laraba yayinda ya tuna da zuwansa na karshe tashar jirgin kasan.

Dan majalisar dattawa ya nemi a kara yawan tarago kan layin Abuja zuwa Kaduna

Dan majalisar dattawa ya nemi a kara yawan tarago kan layin Abuja zuwa Kaduna
Source: UGC

KU KARANTA:Rikicin Zamfara: Rudunar sojin sama ta kashe yan bindiga 20 a dajin Zamfara

Ndume yace, sai da nayi tsayuwar sa’o’i biyu a cikin jirgin kasan yayinda yake tafiya daga dake Abuja zuwa Kaduna. Yace an bashi katin tsayuwane sakamakon karewar katin lambar farko da kuma na kowa da kowa.

A kudurinsa na wannan bukata wanda ya sanya ma taken ‘bukatar kara yawan tarago na gaggawa kan layin dogo na Abuja-Kaduna’, yace mutane da dama masu kaiwa da komowa tsakanin Abuja da Kaduna sun sauya zuwa bin taragon saboda yafi kwanciyar hankali.

Wannan ya biyo bayan dalilin kasancewar hanyar mota tsakanin Kaduna zuwa Abuja ta koma dandalin yan fashi da kuma masu garkuwa da mutane.

Sanatan yayi korafin cinkoson da ake samu wurin sayen katin hawa jirgin kasan. “Abinda sai mai karfi ke iya samu saboda muguntar masu sayar da katin na cewa wanda yafi biyan kudi mai yawa shi zasu sayar ma.” Inji Ndume.

Da dama daga cikin sanatoci sun goyi bayanshi akan wannan kuduri, inda sanata Shehu Sani ke cewa hanyar Abuja-Kaduna na daya daga cikin hanyoyi mafi hadari dake Najeriya a yanzu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel