Ta yaya za ka kwatanta mu da Miyetti Allah – Afenifere, Ohaneze Ndigbo sun caccaki Garba Shehu

Ta yaya za ka kwatanta mu da Miyetti Allah – Afenifere, Ohaneze Ndigbo sun caccaki Garba Shehu

- Kungiyoyin Ohaneze Ndigbo da na Afenifere sun caccaki hadimin shugaban kasa, Garba Shehu

- Sun bukace shi da kada ya sake kwatanta su da kungiyar Miyetti Allah

- A cewar kungiyoyin su basa kashe-kashe da garkuwa da mutane

Kungiyoyin Ohaneze Ndigbo da na Afenifere sun bukaci Garba Shehu, babban hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya alakanta su da kungiyar Miyetti Allah.

Kungiyoyin sun bayyana cewa Miyetti Allah kungiya ce ta makasa kuma suna da hannu a sace-sacen mutane, wanda su basu aikata ba.

Shehu a hira da talbijin din Channels a ranar Talata, 7 ga watan Mayu ya bukaci yan Najeriya da kada suyi wa kungiyar Miyetti Allah kallon yan fashi ills Kungiyar al’ada kamar Afenifere da Ohaneze Ndigbo.

Ta yaya za ka kwatanta mu da Miyetti Allah – Afenifere, Ohaneze Ndigbo sun caccaki Garba Shehu

Ta yaya za ka kwatanta mu da Miyetti Allah – Afenifere, Ohaneze Ndigbo sun caccaki Garba Shehu
Source: Twitter

Da take martani ga furucin, Ohaneze yayin da take zantawa da manema labarai ta nuna rashin amincewa da Shehu inda ta bayyana cewa kungiyar da aka sani a Matsayin na arewa shine kungiyar dattawan arewa.

Kakakin Ohaneze, tace babu adalci wajen kwatanta kungiyar Ohaneze da na ta’addanci.

KU KARANTA KUMA: Zanga-zanga a gidan minista: 'Yan daba sun tarwatsa mambobin NLC

Haka zalika, Yinka Odumakin, kakakin kungiyar Afenifere ya nuna rashin amincewa da fadar shugaban kasa cewa kungiyarsu bata sace da kisan mutane kamar yadda Miyetti Allah ke yi.

Ya bayyana alakanta kungiyoyin a matsayin rashin adalci da abun bakin ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel