Zan hanzarta sa ma dokar kirkirar masarautu hannu da zarar an gabatar da ita – Ganduje

Zan hanzarta sa ma dokar kirkirar masarautu hannu da zarar an gabatar da ita – Ganduje

- Wannan ita ce bukatar mutanen mu mai farin jinni. Hakan kuma zai je tare da kawo cigaba a wannan jihar cikin sauri

- A shirye nake da in sa hannu don ya zama doka ba tare da wani bata lokaci ba.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, yayi alkawarin sa ma dokar dake neman kirkirar karin masarautu hudu masu daraja ta daya a jihar da zarar an gabatar masa da ita.

Ganduje ya adi hakan ne ranar Larba a wurin wani taron manema labarai kafin a fara taron majalisar zartarwar jihar na 136, a dakin taron dake fadar gwanatin Kano.

Yace “Mun ji labarin wani kudurin da aka aika wa Majalisar Dokokin Jiha, ana bukatar da su yi dokar da za ta bada damar kirkirar sarakuna hudu daga masarautar Kano. Mun tabbata wadanda suka gabatar da kudirin sun yi shi ne da kyakkyawar manufa. Kuma suna son cigaban jihar.”

KU KARANTA: Masarautun Kano: Dan majalisa mai wakiltar Dambatta ya fice daga zaman majalisa

“Ina fatar sashen majalisa zai yi aiki kan wannan bukata kuma su gabatar da ita gare ni don sa hannu wanda a shirye nake da in yi don ya zama doka ba tare da wani bata lokaci ba.”

“Wannan ita ce bukatar mutanen mu mai farin jinni. Hakan kuma zai je tare da kawo cigaba a wannan jihar cikin sauri.’

Ganduje yace wannan shawarar ta dade, “Da kirkirar Karin masarautu, kowane bangare na rayuwar al’umma zai inganta.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel