Zanga-zanga a gidan minista: 'Yan daba sun tarwatsa mambobin NLC

Zanga-zanga a gidan minista: 'Yan daba sun tarwatsa mambobin NLC

Wasu 'yan daba da ake kyautata zaton yaran minsitan kwadago da samar da guraben aiyuka, Chris Ngige, ne sun kai wa mambobin kungiyar kwadago ta kasa (NLC) farmaki yayin da suke zanga-zangar nuna fushin su a kan gazawar ministan wajen kafa mambobin kwamitin zartar wa na hukumar NSITF (National Social Insurance Trust Fund).

Kungiyar kwadago ta dade tana matsa wa ministan lamba a kan ya gaggauta daukan matakan rantsar da kwamitin mambobin zartarwa na NSITF da Frank Kokori ke shugabanta.

Da yake nuna bakin cikinsa a kan abinda ya faru, shugaban kungiyar kwadago na kasa, Ayuba Wabba, ya ce 'yan raunata mambobin kungiyar su da dama, ya kara da cewa an garzaya da wadanda suka samu raunin zuwa babban asibitin kasa dake Abuja.

Wabba ya bayyana abinda ya faru a matsayin ta'addanci, ya ce: "wannan ta'addanci ne, an yi amfani da karfi a kan ma'aikata. An yi amfani da harsashin bindiga a kan su.

Zanga-zanga a gidan minista: 'Yan daba sun tarwatsa mambobin NLC
Ministan kwadago; Chris Ngige
Source: UGC

"Sun zo dauke da makamai. yanzu haka maganar da nake yi, mambobin mu hudu na can asibiti sakamakon raunukan da suka samu daga harbin bindiga. Sun zo da yawan su kamar yadda zaku iya gani, amma mu ma gobe zamu kira dukkan mambobin mu su fito wurin zanga-zangar.

"Za mu shiga babbar zanga-zanga. A maimakon ya kare mu, adawa yake da mu. A saboda haka babu amfanin mu tsagaita da zanga-zanga, matukar ba shugaban kasa ne ya saka baki ba, za mu cigaba da zanga-zanga.

DUBA WANNAN: Tsaro: Buhari ya rantsar da wani kwamitin mutum 14 domin inganta tsaron cikin gida

"Ba a taba samun wani lokaci da ma'aikatar kwadago ta dauko 'yan daba su kai wa ma'aikata farmaki ba. Ba a ma taba jin labarin hakan ta faru ba.

"Yanzu mun zo har ofishinsa domin nuna masa rashin jin dadin mu a kan abinda ya faru, dole shugaban kasa ya gaggauta daukan mataki a kan abinda ya faru.

"Ma'aikata sun goya wa shugaban kasa baya. Ngige bashi da ikon da shugaban kasa keda shi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel