Mutum 11 sun mutu, da dama sunyi gudu daga muhallansu, sakamakon harin da makiyaya su kai kauyen Taraba

Mutum 11 sun mutu, da dama sunyi gudu daga muhallansu, sakamakon harin da makiyaya su kai kauyen Taraba

-Rikicin makiyaya yayi sanadiyar mutuwar mutum 11 a jihar Taraba

-Rikici ya fara ne tun kwanaki hudu da suka gabata, a cewar wani mazaunin kauyen da abin ya faru

Mazauna kauyukan Murbai, Kisbap, Sembe da Yawai kauyukan dake karamar hukumar Jalingo ta jihar Taraba sun fadi ranar Laraba cewa mutane 11 ne suka mutu inda da dama suka jikkata sanadiyar harin da wasu makiyaya suka kawo masu a kauyukansu.

Daya daga cikin mazauna kauyen mai suna Cyprian Kamai yace rikici ya fara ne tun kwanaki hudu da suka wuce inda wani maikiwon shanu ya shiga gonar wani mutum domin yin kiwo, da mai wannan gona yayi yinkurin dakatar da makiyayin kawai sai ya daba mashi wuka ya kashe shi.

Mutum 11 sun mutu da dama sunyi hijira daga mazauninsu, sakamakon harin da makiyaya su kai kauyukan Taraba

Mutum 11 sun mutu da dama sunyi hijira daga mazauninsu, sakamakon harin da makiyaya su kai kauyukan Taraba
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Yanzun nan: Buhari ya kaddamar da hukumar cigaban arewa maso gabas (NEDC)

Yinkurin shugabannin yankin na kwantar da tarzoma baiyi wani alfanu ba saboda tuni makiyaya sukayi gangami inda suka farma kauyukan Murbai, Kisbap da sauransu, al’amarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Kamai yace daruruwan mutanen da rikici ya shafa sun gudu daga mazauninsu inda suka kasance a matsayin yan gudun hijira. Yanzu haka suna makarantar firamare ta Nunkai a Jalingo.

“ Masu gudun hijirar na bukatar taimako daga wurin gwamnati. Agaji suke nema domin rage zafin halin da suka tsinci kansu.” Inji Kamai.

Rebecca Awoshiri wacce ta zanta da wakilin jaridar Punch a sansanin yan gudun hijira na Nukkai tace mutum 5 aka kashe a Murbai yayinda 6 kuma an kashesu ne a Sembe.

Shi kuma jami’in hulda da jama’a na yan sandan jihar DSP David Misal, da yake tabbatar da aukuwar wannan lamarin cewa yayi mutum 6 ne kadai aka kashe yayinda aka raunata mutane da dama.

“ Mun tura da jami’anmu kauyukan da wannan abu ya shafa. Kuma a daidai wannan lokacin da nake magana daku mataimakin kwamshinan yan sanda na tsaye kan kafafunsa domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.” Inji David.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel