Ka fuskanci matsalar tsaro a Kaduna ka rabu da shuwagabannin mu – Yarbawa ga El-Rufai

Ka fuskanci matsalar tsaro a Kaduna ka rabu da shuwagabannin mu – Yarbawa ga El-Rufai

Kungiyar matasan kabilar Yarbawa ta duniya gaba daya ta gargadi gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai daya kiyayi duk wani abinda zai iya janyo masa jin kunya daga kabilar Yarbawa, kamar yadda shugabanta, Aremo Oladotun Hassan ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Hassan na cewa rahoton da aka watsa a kwanakin baya inda El-Rufai ke cewa zai koya ma yan siyasar jahar Legas yadda ake karya lagon iyayen gidan siyasa ba wani abu bane illa cin mutunci ga jama’a Yarbawa.

KU KARANTA: Abin kunya: An kaure da dambe a zauren majalisa, an karairaya sandan iko

A cewar Hassan, El-Rufai bashi da ikon yin wadannan kalamai a kasar Yarbawa, kamata yayi ya fuskanci matsalolin tsaro da fargaba da suka dabaibaye jahar Kaduna, ba wai ya dinga ma Yarbawa katsalandan a lamarin daya shafesu ba.

“Duk da yace ya kawo karshen siyasar ubangida a Kaduna, har yanzu bamu ga amfanin hakan ga al’ummar jahar ba, ba kamar jahar Legas ba inda siyasar ubangida tayi mana riga tayi mana wando ba, siyasar ubangida ce ta kai ga samar da jam’iyyar APC, har ta kai ga Buhari ya zama shugaban kasa, wanda shi kuma ya taimaki El-Rufai ya zama gwamna.

“Siyasar ubangida tayi mana rana, tunda ta mayar da Legas babbar cibiyar kasuwanci ta duniya, kuma cibiyar tattalin arziki mafi girma na biyar a nahiyar Afirka gaba daya. Siyasar ubangida a Legas ta samar da kwararrun jami’an gwamnati dake rike da mukamai daban daban a gwamnatin Najeriya.

“Siyasar ubangida ta sanya jahar Legas kasancewa jaha daya tilo dake da karfin ikon tsayawa da kafarta ba tare da neman agajin gwamnatin tarayya ba, don haka ba zamu zura ido ba wani yazo ya nemi ya zagi shuwagabanninmu ba.” Inji shi.

Daga karshe Hassan ya caccaki El-Rufai da cewa dama yayi kaurin suna wajen tayar da zauni tsaye tare da rura rikicin kabilanci dana siyasa, kamar lokacin da yayi maganan zuba gawarwaki a cikin jakkuna gabanin zaben 2019 da ire iren wadannan furuci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel