Cuwa-cuwa wajen bayar da kwangila ne ummul aba'isin rashin kammala ayyuka

Cuwa-cuwa wajen bayar da kwangila ne ummul aba'isin rashin kammala ayyuka

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa ta ce za tabi duk wata hanya da ta dace domin ganin ta kawo karshen cuwa-cuwar da ake tafkawa a wurin bayar da kwangila a kasar nan

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa ta ce cuwa-cuwa da masu karbar kwangila ke yi a kasar nan ita ce ummul aba'isin rashin kammala wasu ayyuka a kasar nan.

Da ya ke jawabi a yayin wani taro jiya Talata a Abuja, shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai rikon kwarya, Ibrahim Magu, ya ce biyan kudin kwangila, wanda idan an bawa kamfani kwangila za a bukaci ya biya wani kashi a cikin kudin aikin, babbar matsala ce da ya kamata a daina amfani da ita.

Cuwa-cuwa wajen bayar da kwangila ne ummul aba'isin rashin kammala ayyuka

Cuwa-cuwa wajen bayar da kwangila ne ummul aba'isin rashin kammala ayyuka
Source: Depositphotos

Mrs. Enakeno Oju, wacce ta wakilci shugaban hukumar, ta bayyana cewa adadin kudin da ake karba bayan kamfanin da aka bai wa kwangila ya kammala biyan wani bangare na kudin kwangilar, ba ya isa a gabatar da aikin da aka bayar.

"Akwai lokuta da dama da ba a aiwatar da aiki. Saboda haka ba za mu iya cigaba da wannan tsarin ba. Saboda hakan alama ce da ke nu na cewa cin hanci ya shiga cikin tsarin, kuma dole mu kawo karshen duk wani cin hanci a kasar nan."

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: An yiwa Sarki yankan rago a jihar Sokoto

Shugaban kungiyar ACCI, Prince Adetokunbo Kayode, ya ce an kafa cibiyarta su ne don taimakawa jam'iyyu da ke karbar kwangila don magance matsaloli na kasuwanci.

Kayode ya ce, "yarjejeniya, sulhu sasantawa da duk wasu nau'o'i da za a daidaita an amince da su a matsayin hanyar da ta dace don warware yarjejeniyar kwangilar gwamnati."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel