Obasanjo ya maka jaridar Punch a kotu

Obasanjo ya maka jaridar Punch a kotu

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya maka jaridar The Punch a gaban kotu, sannan ya nemi diyyar bata masa suna da zubar masa da mutunci da jaridar ta yi.

Obasanjo na neman diyya ce a kan jaridar ta The Punch da kuma wani fitaccen marubucin ta na mako-mako, wato Sola Olumhense.

Ya na neman a biya shi zunzurutun kudi har naira bilyan daya, saboda nauyi da munin cin mutuncin da ya ce an yi masa.

Ya kai karar ne a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, game da rubutun da Sola Olumhense ya yi a kan sa, a ranar 17 ga watan Janairu, 2019.

Obasanjo ya maka jaridar The Punch a kotu

Obasanjo ya maka jaridar The Punch a kotu
Source: UGC

Rubutun mai taken, “Wannan ce iyakar gudummawar da Obasanjo zai iya bayarwa”, shi Obasanjon ya ce duk abin da aka rubuta a kan sa ba gaskiya ba ne.

Obasanjo ya ce: ”Jaridar Punch ta buga karairayin da Sola Olumhensen ya rubuta a kai na, wadanda babu gaskiya a ciki, bata min suna ne, babu hujjoji, cin mutunci ne, zubar min da girma ne, munanan kalamai ne, gilla ce, kuma sun ja jama’a na gudu na tare da tozarta ni.

“A cikin rubutun, Olumhense ya nuna cewa Obasanjo na nuna wa duniya cewa shi mutumin kirki ne, amma ba haka abun ya ke ba.”

Tsakure daga kadan daga rubutun da Olumhense ya yi, ya nuna cewa Obasanjo ya nuna wa duniya cewa ya kafa Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ICPC don hana cin hanci da rashawa, amma ba da wannan manufar ya kafa ta ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kungiyar NLC sun yi wa ministan kwadago ba-ba-ke-re a a kofar gidansa

Ya ce Obasanjo ya kafa EFCC da ICPC ne domin su zame masa karnukan farautar abokan hamayyarsa.

“Sai abin da ya ke so suke yi masa, ba abin da ya dace ya rika yi da hukumomin ba a lokacin da ya ke mulki.”

Olumhense ya ce Obasanjo ya kirkiro batun farautar kudaden da aka ce marigayi Janar Sani Abacha ya wawura ne, don kawai ya yi masa bi-ta-da-kullin daure shi da Abacha ya yi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel