Kashe-kashe, garkuwa da mutane duk jarrabawa ce daga Allah – Limamin Aso Rock

Kashe-kashe, garkuwa da mutane duk jarrabawa ce daga Allah – Limamin Aso Rock

- Babban limamin masallacin fadar Shugaban kasa, Sheik Abdulwaheed Sulaiman, ya bayyana abunda ya kamata yan Najeriya suyi akan yawan kashe-kashe da ayyukan ta’addanci

- Sulaiman a ranar Laraba, 8 ga watan Mayu ya bayyana cewa yan Najeriya su tuba daga zunubansu sannan su roki Allah

- Ya kara da cewa annobar fashi da makami, Kashe-kashe da laifuka duk jarrabawa ce daga Allah

Yawan ayyukan ta’addanci, kashe-kashe das ace-sacen mutane a kasar jarrabawa ce daga Allah kamar yadda babban limamin masallacin fadar Shugaban kasa, Sheik Abdulwaheed Sulaiman, ya bayyana.

Sulaiman ya bayyana cewa domin magance wannan mumunan annoba, yan Najeriya na bukatar tuba daga zunubansu sannan su roki Allah, jaridar The Cable ta ruwaito.

Kashe-kashe, garkuwa da mutane duk jarrabawa ce daga Allah – Limamin Aso Rock

Kashe-kashe, garkuwa da mutane duk jarrabawa ce daga Allah – Limamin Aso Rock
Source: Facebook

Da yake koro jawabin limamin, Garba Shehu, babban hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa Sulaiman “yayi godiya ga Allah madaukakain sarki da ya bari aka yi zabe cikin kwanciyar hankali a fadin kasar”.

“Yayi kira ga komawa ga Allaj sannan a roki Allah kan matsalolin da kasar ke fuskanta. Yace lamarin tsaro jarrabawa ce daga Allah.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotun zaben Shugaban kasa ta fara zama akan karar Atiku, Peter Obi ya hallara

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Atiku Abubakar, dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a ranar Laraba, 8 ga watan Mayu yace Najeriya na bukatar abubuwa uku da zasu taimaka mata wajen magance matsalolin da take ciki a yanzu.

Atiku ya lissafa abubuwan guda uku a matsayin azumi, addu’a da adalci kamar yanda ya dauko daga ayar Al’qurani mai girma dangane da azumin mumini a Musulunci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel