Kungiyar dattawan Arewa ta yi wa Buhari wankin babban bargo kan tsaro

Kungiyar dattawan Arewa ta yi wa Buhari wankin babban bargo kan tsaro

Shugaban kungiyar dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana cewa, matsalar tsaro a yankin arewacin kasar ta fi muni a gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari fiye da lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Ango wanda ya kasance tsohon shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, ya ce, shugaba Buhari ba ya tabuka wani abin azo a gani wajen magance matsalar, jaridar Punch ta rawaito.

Jigon na arewa dai na mayar da martani ne game da tsokacin da hadimin Buhari, Garba Shehu ya yi a yayin zantawa da gidan talabijin na AIT a shirin Kakaaki, in da ya ce, kasancewar shugaban kasar ya fito daga garin Daura, hakan ba ya nufin ba za a iya aikata mummunan laifi a Daura ba ko kuma a ba ta fifiko na musamman.

Kungiyar dattawan Arewa ta yi wa Buhari wankin babban bargo kan tsaro

Kungiyar dattawan Arewa ta yi wa Buhari wankin babban bargo kan tsaro
Source: Twitter

Shehu na magana ne dangane da sace Surukin Buhari, Magajin Gari, Alhaji Musa Uba da ‘yan bindiga suka yi a Daura.

KU KARANTA KUMA: Azumi, addu’a da adalci ne abunda Najeriya ke bukata a wannan lokacin - Atiku

Shehu ya ce, gwamnatin shugaba Buhari na aiki tukuru wajen magance ta’adanci a kasar.

Ko a cikin watan jiya, sai da Kungiyar Dattawan ta ce, za a ci gaba da fama da hare-haren ‘yan bindiga a Zamfara da Katsina da Kaduna da Sokoto muddin ba a tanadi yanayin aiki mai kyau ga jami’an ‘yan sanda ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel