Zababben dan majalisar wakilai na neman diyyar naira miliyan 500 kan bata masa suna

Zababben dan majalisar wakilai na neman diyyar naira miliyan 500 kan bata masa suna

- Honorabul Godday na bukatar kotu ta tilasta ma wanda yake kara da ya fito a lokacin da aka fi kallo da sauraron rediyo ya karyata batancin da yayi masa

- Samuel Godday,yace zargin da aka wallafa karyace zalla wadda aka kitsa don zubarwa da kuma cin mutuncinsa

Zababben dan majalisa mai wakiltar mazabar Apa/Agatu a zaben 23 ga watan Fabrairun 2019 a karkashin jam’iyyar Labour Party (LP), Honorabul Samuel Godday, ya kai karar Mr Morgan Adikwu, wani mai harkar watsa labaran yanar gizo don neman diyyar naira miliyan 500 kan bata masa suna.

An sa karar ne a babbar kotun dake garin Makurdi ta jihar Benue a matsayin martini kan wani zargi na cewa wai Honorabul Samuel Godday ya yi bugin takardarsa ta shaidar kammala karatun digiri a jami’ar Abuja da takardar shaidar dauke wa mutum shiga aikin yi wa kasa hidima (NYSC) wadanda ya gabatar ma Hukumar zabe mai Cin Gashin Kanta ta Kasa (INEC).

A cikin sakon da Morgan ya wallafa ya gabatar da wata takardar da ake zaton ta karya ce wadda yace ta fito daga hannun jami’ar Abuja da hukumar NYSC, wadda ke cewa takardun shaidar da Honorabul Samuel ya gabatar ma hukumar zabe ta kasa ba su suka ba shi ba.Wani abunda bukatar da Samuel ya gabatar ta kunsa shine kotu ta dakatar da wanda ake kara (Mr Morgan Adikwu), da ‘yan korensa daga cigaba da bata ma mai kara suna.

KU KARANTA: Matsalar rushewar gidaje: Jihohin Legas, Anambra da Abuja na kan gaba

Honorabul Godday kuma yana bukatar kotu ta tilasta ma wanda yake kara da ya fito a lokacin da aka fi kallo da sauraron rediyo ya karyata batancin da yayi masa, kafofin watsa labaran da yake bukatar Morgan ya karyata kanshi a cikin su sune hukumar talebijin ta kasa (NTA), Channels Television, African Independent Television, Rediyoo Najeriya, Rediyon jihar Benue, Harvest FM, jaridu biyar dake fitowa kullun da kuma kafofin sadarwar yanar gizo.

Samuel Godday,yace zargin da aka wallafa karyace zalla wadda aka kitsa don zubarwa da kuma cin mutuncinsa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa

Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel