Yanzu Yanzu: Kotun zaben Shugaban kasa ta fara zama akan karar Atiku, Peter Obi ya hallara

Yanzu Yanzu: Kotun zaben Shugaban kasa ta fara zama akan karar Atiku, Peter Obi ya hallara

- Peter Obi, yan siyasa da lauyoyin PDP da na APC sun hallara yayinda kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban kasa ta fara zama

- Shugabar kotun daukaka kara, Justis Zainab Bulkachuwa, ta jagoranci zaman na farko

- Justis Bulkachuwa tayi alkawarin cewa za su bi doka wajen gudanar da shari’an da ke gabansu

Kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban kasa ta fara zamanta na farko a yau, Laraba, 8 ga watan Mayu.

Ana sanya ran kotun zata fara sauraron karan dad an takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, ya shigar akan jam’iyyar All Progressives Congress da dan takararta Shugaban kasa Muhammadu Buhari, da sauaransu.

Daga cikinsu sun hada da lauyoyin mai kara Alhaji Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta Peoples Democratic Party, lauyoyin Shugaban kasa da jam’iyyarsa ta All Progressive Congress da lauyoyin hukumar zabe mai zaman kanta.

Yanzu Yanzu: Kotun zaben Shugaban kasa ta fara zama akan karar Atiku, Peter Obi ya hallara
Yanzu Yanzu: Kotun zaben Shugaban kasa ta fara zama akan karar Atiku, Peter Obi ya hallara
Source: UGC

Haka zalika, dan takarar mataimakin Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party a zaben da ya gudana a ranar 23 ga watan Fabrairu, Peter Obi, ya hallara a kotun.

Jam’iyyar PDP da dan takararta na Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, sun shigar da kara inda suke kalubalantar sakamakon zabe wanda hukumar zabemai zaman kanta ta kaddamar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta All Progressives Congress a matsayin masu nasara.

KU KARANTA KUMA: Ban kamu da kowani ciwon zuciya ba - Abokin takarar Atiku, Peter Obi

Justis Zainab Bulkachuwa ce za ta jagoranci majalisar kotun mai dauke da mutum biyar.

Tace kotun za ta yi aiki daidai da doka sannan za a saurari karar ne rana daya bayan daya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel