Azumi, addu’a da adalci ne abunda Najeriya ke bukata a wannan lokacin - Atiku

Azumi, addu’a da adalci ne abunda Najeriya ke bukata a wannan lokacin - Atiku

Atiku Abubakar, dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a ranar Laraba, 8 ga watan Mayu yace Najeriya na bukatar abubuwa uku da zasu taimaka mata wajen magance matsalolin da take ciki a yanzu.

Atiku ya lissafa abubuwan guda uku a matsayin azumi, addu’a da adalci kamar yanda ya dauko daga ayar Al’qurani mai girma dangane da azumin mumini a Musulunci.

KU KARANTA KUMA: Buhari da APC ne ya kamata su dauki alhakin rashin tsaro – Atiku

Legit.ng ta rahoto a baya yanda tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar, yayi jawabi ga musulman Najeriya wadanda suka azumci watan Ramadana.

A sakonsa na ranar 17 ga watan Yuli, Atiku ya bukaci al’umma da su gudanar da addu’o’i don zaman lafiya a kasar wacce ke fuskantan kalubale a fannin tsaro.

A wani jawabin da hadiminsa ya gabatar a Abuja, dan siyasan ya bayyana rashin jin dadin shi bisa rikici dake tashi a ko da yaushe, wanda hakan ya zamo barazana ga zaman lafiyan kasar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kungiyar NLC sun yi wa ministan kwadago ba-ba-ke-re a a kofar gidansa

Atiku ya bayyana cewa shuwagabannin musulmai suyi iya kokarinsu wajen ganin an kau da masu tsatsauran ra’ayi a al’umman musulmai.

Turakin Adamawan yayi korafin cewa yan Najeriya sun zamo masu zaman dar-dar saboda tsoron matakan yan ta’adda. Har ila yau yayi kiran gaggawa da a daukaka hari akan asalin ta’addanci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel