Makarantar horar da jami’an hukumar kiyaye hadurra (FRSC) za ta fara koyar da karatun digiri

Makarantar horar da jami’an hukumar kiyaye hadurra (FRSC) za ta fara koyar da karatun digiri

- “Muna fatar samun yardar fara koyar da karatun digiri nan da watan Satumba daga hukamar kula da jami’o’i ta kasa”

- “Tashar rediyon kiyaye dokar hanya za ta fara aiki a karshen wannan watan ko farkon watan Yuni.

Makarantar horar da jami’an hukumar kiyaye hadurra (FRSC) dake garin Udi ta jihar Enugu za ta fara bayar da takardun shaidar karatun digiri a cikin watan Satumbar wannan shekarar, kamar yadda shugaban hukumar Mr Boboye Oyeyemi ya sanar a Abuja, ranar Talata.

Oyeyemi yace hukumar kiyaye hadurra FRSC na kokari matuka na ganin cewa an daga darajar makarantar zuwa makarantar dake bayar da takardun shaidar karatun digiri.

“Muna fatar samun yardar fara koyar da karatun digiri nan da watan Satumba daga hukamar kula da jami’o’i ta kasa”

“Za mu fara sayar da takardun shiga karatun digirin a cikin watan Ogusta idan mun samu yardar Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa. Muna da makarantu biyu da za mu shirya a cikin shekaru biyu masu zuwa, muna bukatar makarantar horaswa don amfanin kananan ma’aikatanmu, kuma muna bukatar Kwalejin horas da manyan ma’aikatanmu"

A maganar tashar rediyon kiyaye dokar hanya da hukumar FRSC ta gina, Oyeyemi yace za a fara gudanar da aikin gwaji cikin wata mai zuwa.

KU KARANTA: Buhari yayi juyayin rashin wata ‘yar siyasar dake matukar mara masa baya

“Tashar rediyon kiyaye dokar hanya za ta fara aiki a karshen wannan watan ko farkon watan Yuni. Za mu fara aikin gwaji kafin kaddamarw da ita, muna kan gaba ta karshe. Mun samu mitar da za mu rika watsa shiye-shiryenmu a kanta, muna jiran zuwan kayan aiki ne a halin yanzu.”

Oyeyemi yace an kammala ginin tashar rediyon, kuma mutanen da aka dauka don tafiyar da watsa shirye-shiryen tashar a halin yanzu suna karbar horo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa

Mun gode da kasancewarku tare da mu. Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel