Yanzu Yanzu: Kungiyar NLC sun yi wa ministan kwadago ba-ba-ke-re a a kofar gidansa

Yanzu Yanzu: Kungiyar NLC sun yi wa ministan kwadago ba-ba-ke-re a a kofar gidansa

- Mambobin kungiyar kwadago sun kai mamaya gidan ministan kwadago da diban ma’aikata, Chris Ngige

- Masu zanga-zangar sun yi masa babakere a kofar shiga gidan nasa da ke Abuja

- Sun gudanar da zanga-zangan ne akan zargin gazawar ministan wajen rantsar da Frank Kokori a matsayin Shugaban hukumar NSITF

Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta mamaye gidan ministan kwadago da diban ma’aikata, Chris Ngige sannan suka yi ba-ba-ke-re a mashigin gidansa da ke babbar birnin tarayya, Abuja.

Kungiyar sun dauki wannan matakin ne akan zargin gazawar ministan wajen rantsar da Frank Kokori a matsayin Shugaban hukumar inshoran zamantakewa na Najeriya (NSITF).

Yanzu Yanzu: Kungiyar NLC sun yi wa ministan kwadago ba-ba-ke-re a a kofar gidansa

Yanzu Yanzu: Kungiyar NLC sun yi wa ministan kwadago ba-ba-ke-re a a kofar gidansa
Source: UGC

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, ba a riga an san ko ministan ya magance matsalar kungiyar kwadagon da ke zanga-zanga ba.

KU KARANTA KUMA: Fadar Shugaban kasa: Miyetti Allah ma kungiya ce kamar ta Ohanaeze Ndigbo da Afenifere

Yanzu Yanzu: Kungiyar NLC sun yi wa ministan kwadago ba-ba-ke-re a a kofar gidansa

Sun gudanar da zanga-zangan ne a gidan ministan da ke Abuja
Source: UGC

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana juyayinsa game da rasuwar Hajiya Hindu Ja’afaru Danmalam, wadda take mai matukar goyon bayan shugaban kasar ce tun farkon gwaggwarmayar siyasarsa.

Kamar yadda wata takardar bayanin da mai magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu ya raba ma manema labarai take cewa, shugaban kasa a cikin wani sakon da ya aika ma iyalan marigayiya Hindu Danmalam, da Sarkin Kano, da gwamnatin jihar Kano yace zai yi kewar Hjiya Hindu wadda tayi tsayin daka wurin kare shi da gwamnatinsa a duk lokacin bukatar hakan ta taso, koda kuwa a lokacin da ta hadu da tursasawar manyanta a gidan siyasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel